012 TAQAITACCEN BAYANI AKAN AURE, SAKI, BIKO, ZIHARI, I'LA'I, LI'ANI, KUL'I, DA KUMA SHAYARWA

kashi na goma-sha-biyu
@@@@ @@@@ @@@@ @@@@
بسم الله الرحمن الرحيم
والصلاة والسلام على أشرف أنبياء سيدنا ومولانا محمد النبي، وعلى أزواجه أمهات المؤمنين وذريته وأهل بيته الطاهرين وصحابته الأكرمين وعلينا معهم أجمعين
@@@@ @@@@ @@@@ @@@@

Ina Qara Godewa Allah Bisa Kasantuwar Musulunci Addinina, Annabi Muhammad SAW Annabi Na, Al-qur'ani Da Hadisi Littatafaina Tsarkaka, Ka'aba Ash-sharifah Alqiblata, Malikiyyah Mazhabata, Ash'ariyyah Aqidata Ta Sunnah,  Hausa Qabilata.

Aslm
Ya 'Yan,uwana Musulmai Maza Da Mata Manya Da Qanana Da Fatan Kowa Yana Qoshin Lafiya, Marasa Lafiyanmu Na Gida Da Na Asibiti Ubangiji Allah Ya Basu Lafiya, Masu Lafiya Kuma Allah Ya Qara Musu Lafiya, Iyayenmu Da Kakanayenmu Yayyunmu Da Qannanmu, Da Suka Rigamu Gidan Gaskiya Ubangiji Allah Yaji Qansu Yayi Musu Rahma, Muma In Tamu Tazo Allah Ya Sa Mu Cika Da Imani.
Ameen Summa Ameen
*** *** ***    *** *** ***    *** *** ***

A Gurguje Insha Allahu Zamu 'Dan Ta6a Bayani Akan AURE, SAKI ETC Daga /raubabangida/ Littafin Da Ake Qira Da RISALA Wanda Abu Muhammad Abdullahi Bini Abiy Zaideen Al-Qirawaniy RH Ya Wallafa

In Bamu Manta Ba, A Kashi Na Goma, Munce Insha Allahu Zamu Tashi A Inda /raubabangida/ Malam Yake Cewa :

وَلِلْمَرْأَةِ أَنْ تَفْتَدِيَ مِنْ زَوْجِهَا بِصَدَاقِهَا أَوْ أَقَّلَ أَوْ أَكْثَرَ إِذَا لَمْ يَكُنْ عَنْ ضَرَرِ بِهَا،
Mace Tana Iya Fansan Kanta Daga Mijinta /raubabangida/ Da Sadakinta, Ko Abunda Yayi Qaranci Ko Yayi Yawa, Idan Ya Kasance Hakan Bazai Cutar Dashi Ba.
( Abunda Nufi : Idan Mace Taga Ta Gaji /raubabangida/ Da Zama Da Mijinta, Tana Iya Daukan Wani Abu Daga Kudi Ko Qadara Ta Bashi Tace Ga Wannan Ni Gaji Da Zama Da Kai, Kaje Kayi Wani Auren, Wannan Abun Da Zata Bayar Shine Ake Qira Da KUL'I, Hakan Yana Biyo Bayan Misali Idan /raubabangida/ Mijin Yana Da Wasu 'Dabi'u Da Matar Tayi-Tayi Ya Daina Ya Qi Ya Daina.
Ko Kuma Misali Baya Iya Biya Mata Buqata Na Aure, Tana Tsoron  Karta Taje Ta Sa6awa Allah, Shi Kuma Mijin Yayi Iya Yinsa Amma Abun Yaqi, Da Tayi Masa Terere A Duniya, Sai Tayi Kul'i.
Kuma /raubabangida/ Haka Kawai Taji Ta Gaji Da Zama Dashi, Sai Tayi Masa Kul'i Dade Makamantansu )

 ( Wajen Bada Kudin Misali Idan Mijin Ya /raubabangida/ Biya Sadaki ₦200,000.00, Idan Tana Da Hali Tana Iya Bashi Sama Da Hakan Idan Hakan Bazai Cutar Da Ita Ba,
Idan Kuma Zai Cutar Da Ita, Tana Iya Bayar Da Qasa Da Haka )


فَإِنْ كَانَ عَنْ ضَرَرَ بِهَا رَجَعَتْ بِمَا أَعْطَتْهُ وَلَزِمَهُ الْخُلْعَ.
Idan Hakan Ya Kasance Zai Cutar Da Ita, Sai Ta Dawo Da Abunda Ta Bayar, ( Duk /raubabangida/ Abunda Matar Ta Bawa Mijin Da Sunan Kul'i, Da Zarar Mijin Ya Sa Hannu Ya Kar6a ) Toh Kul'i Ya Tabbata Gareshi.


وَالْخُلْعُ طَلْقَةُُ لاَ رَجْعَةَ فِيهَا إٓلاَ بِنَكَاحِ جَدِيدِِ بِرِضَاهَا.
Shi Kuma Kul'i Saki Ne Da Babu Biko/Kome A Cikinsa, Sai Dai Da Sabon Aure, Da Kuma Yardanta Ita Matar.
( Da /raubabangida/ Zarar Kul'i Ya Faru Toh Saki Ya Afku, Idan Kuma Matar Ta Koma Gidansu Babu Daman Yin Biko/Kome, Sai Dai Idan Matar Da Mijin Sun Dai-Daita Kansu Sai A Sake Daura Musu Sabon Aure )

Domin Dan Qarin Bayani Akan Kul'i Jeka
MUWADDA MALIK
29 - KITABUL DALAQ
11 - BABU MA JA'A FIL KUL'I
HADISI NA 1198 DA NA 1199
Zaku /raubabangida/ Ga Hadisai Guda Biyu, Dangane Da Hakan, Hadisan Suna Da 'Dan Tsayi.
*

وَالْمُعْتَقَةُ تَحْتَ الْعَبْدِ لَهَا الْخِيَارُُ أَنْ تُقِيمَ مَعَهُ أَوْ تُفَارِقَهُ.
Baiwar Da Take Qarqashin Bawa ( Take /raubabangida/ Auren Bawa ) Ta Samu 'Yanci, Aka 'Yantata, Toh Tana Da Za6i, Inta Ga Dama Da Zauna A Tare Dashi, Inta Ga Dama Rabu Dashi ( A Raba Auren )
( Amma Inda Soyayya, Soyayya Ta Gaskiya /raubabangida/ Bazata So A Rabasu Ba, Wanda In Akayi Haquri Nan Gaba, Shima Zai Samu 'Yanci )
*

وَمَنِ اشْتَرَى زَوْجَتَهُ انفَسَخَ نِكَاحُهُ
Wanda Ya Sayi Matarsa, Aurensu Ya 'Baci
( Hakan Yana Faruwa Ne, A Zamanin Da, Zamanin Yaqe-Yaqe, Wanda Za'a Zo Gari Aci Gari Da Yaqi /raubabangida/ Akama Mutane Ribatattun Yaqi, Toh Wanda Aka Kama Matarsa A Ribar Yaqi, Maqayan Sukazo Suna Bada Fansar Ribatattun Ko Sayar Da Ribatattun Yaqi, Sai Ka Zo Kaga Matarka A Wannan Halin, Ka Fansheta Ko Ka Sayeta Malam Yace Aurenku Ya Baci, Saboda A Da Matarka Ce, Yanzu/raubabangida/ Kuma Ka Sayeta, Matsayinta Yanzu Ya Koma Kamar Baiwa, Domin Warware Wannan Matsalar Ku Tuntu6i Malaman Sunnah Masu Karantar Da Al-qur'ani Da Hadisi, Ba Malaman /raubabangida/ Tsibbu Ba )


وَطَلاَقَ الْعَبْدِ طَلَقَتَانِ، وَعِدَّةُ الأَمَةِ حَيْضَتَانِ.
Sakin Bawa Saki Biyu Ne ( Wato : Limit Iyakar Adadin Saki Da Mutum Bawa Yake Da Dama, Shine Saki Biyu /raubabangida/ Idan Bawa Ya Saki Matarsa Sau Biyu Toh Ta Ku6uce Masa, Bashi Da Damar Yin Biko/Kome Sai Tayi Wani Auren Ta Fito, Auren Ma Ba Auren Sakin Wuta Ba )
Hakan Iddan Mace Baiwa, Idda Biyu Ne ( Mace Baiwa Idan Mijinta Ya Saketa, Toh Jini Biyu Period Time Biyu Zatayi, Kafin Tayi Jini Biyu Idan Mijin Ya Dawo Da Ita Ta Koma, Amma Idan /raubabangida/ Ta Wuce Jini Biyu, Toh Mijin Sai Dai Ayi Sabon Aure, Hakanan Takaba Ga Baiwa Wata Biyu Ne Da Kwana Biyar, Ita Bazata Yi Wata Hudu Da Kwana Goma /raubabangida/ Ba )
*

وكَفَّارَاتُ الْعَبْدِ كَالحُرِّ بِخَلاَفِى مَعَانِى الْحُدُودِ وَالطَّلاَقِ.
Yin Kaffara Ga Mutum Bawa ( Ko Baiwa Duka ) Daya Ne Da Na Mutum 'Yantatce, Sa6anin Ma'ana Na Iyakoki ( Sauran Hukunce-Hukunce ) Da Hukuncin Saki.
( Wato : Misali Idan Bawa Ko Baiwa Suka Karya Azumi Da Gangan, Yadda /raubabangida/ 'Da 'Yantatce Zaiyi Azumin Kaffara Wata Biyu A Jere, Haka Bawa Ko Baiwa Zatayi )
*

Masha Allah Alhamdulillahi
Duka-Duka Anan Zamu Tsaya Da Izinin /raubabangida/ Allah, Insha Allahu Kuma A Kashi Na Sha-Biyu Kuma Na Qarshe Zamu Tashi A Inda Malam Yake Cewa :
وَكُّلُ مَا وَصَلَ إِلَى جَوفِ الرَّضِيعِ فِى الْحَوْلَينِ

Ina Mai Cewa
Abunda Muka Rubuta Dai-Dai Ubangiji Allah Ya Bamu Ladansa, Abunda /raubabangida/ Muka Rubuta Bisa Kuskure Ubangiji Allah Ya Yafe Mana.

07 Jumada Awwal 1448 Hijrah
18 October 2026 Miladiyya
Ranar Lahadi

marubuci
Abu Maryam Muhammad Rabiu Babangida el-Jimetawiy Bini Alhaji Umar al-Auyowiy Bini Muhammad Bini Haruna

( Wanda Aka Fi Sani Da )

@raubabangida
Rabiu Alhaji Umar Babangida
BPM, PAA, PAN, PHM, MVM, AUYO, YOLA-NORTH

Comments

Popular posts from this blog

TAQAITACCEN TARIHIN DAULAR AUYO

HAPPY BIRTHDAY TO YOU OUR DEAR FATHER, 13 APRIL

YAU SHEKARA GOMA DA RASUWA MAMANA