TAQAITACCEN TARIHIN RAYUWAR BUHARI DA MULKISA
008 - 016
MAJOR GENERAL MUHAMMADU BUHARI ARDO ADAMU
MULKINSA NA SOJA DA NA FARIN HULA
@@@@ @@@@ @@@@ @@@@
بسم الله الرحمن الرحيم
والصلاه والسلام على أشراف أنبياء سيدنا ومولانا محمد النبي وعلى أزواجه أمهات المؤمنين وذريته وأهل بيته الطاهرين وصحابته الأكرمين وعلينا معهم أجمعين
@@@@ @@@@ @@@@ @@@@
Ina Qara Godewa Allah Bisa Kasantuwar Musulunci Addinina, Annabi Muhammad SAW Annabi Na, Al-qur'ani Da Hadisi Littatafaina Tsarkaka, Ka'aba Ash-sharifah Alqiblata, Malikiyyah Mazhabata, Ash'ariyyah Aqidata Ta Sunnah, Sufanci Matafiyata, Qadiriyyah Dariqata, Hausa Qabilata.
Aslm
Ya 'Yan,uwana Musulmai Maza Da Mata Manya Da Qanana Da Fatan Kowa Yana Qoshin Lafiya, Marasa Lafiyanmu Na Gida Da Na Asibiti Ubangiji Allah Ya Basu Lafiya, Masu Lafiya Kuma Allah Ya Qara Musu Lafiya, Iyayenmu Da Kakanayenmu Yayyunmu Da Qannanmu, Da Suka Rigamu Gidan Gaskiya Ubangiji Allah Yaji Qansu Yayi Musu Rahma, Muma In Tamu Tazo Allah Ya Sa Mu Cika Da Imani.
Ameen Summa Ameen
*** *** *** *** *** *** *** *** ***
Muhammadu Buhari Tsohon Soja Ne Kuma 'Dan Siyasa A Najeriya Wanda Yayi Mulkin /raubabangida/ Qasar Sau Biyu: A Matsayin Shugaban Kasar Soja ( 1983–1985 ) Da Kuma Matsayin Shugaban Qasa Na Farar Hula ( 2015–2023 ).
Ga Taqaitaccen Tarihin Rayuwarsa Da Kuma Lokacin Mulkinsa:
1 - Rayuwarsa Ta Fari Da Aikin Soja
Aifuwa : An Haife Shi A Ranar 17 Ga Disamba, 1942 A Garin Daura Da Ke Jihar /raubabangida/ Katsina.
Aikin Soja : Ya Shiga Aikin Sojan Najeriya A Shekarar 1961, Inda Ya Halarci /raubabangida/ Makarantun Horar Da Sojoji Daban-Daban A Najeriya, Birtaniya, Da Amurka.
Muqanai Da Ya Rike: Ya Rike Mukamai Daban-Daban A Aikin Soja, Ciki Har Fa Kasancewarsa Gwamnan Jihar Arewa Maso Gabas ( North-Eastern State ) Da Kuma /raubabangida/ Ministan Man Fetur A Shekarun 1970.
2 - Mulkinsa Na Farko ( Sojan Soja: 1983 – 1985 )
Kar6ar Mulki : Ya Karbe Mulki Ta Juyin Mulkin /raubabangida/ Soja A Ranar 31 Ga Disamba, 1983, Bayan Cire Gwamnatin Farar Hula Ta Shehu Shagari.
Manufofi Da Tsare-Tsare:
Yaqi Da Karbar Hanci Da Rashawa: Ya Qaddamar Da Shirin War Against Indiscipline ( WAI ) Domin Dawo Da Tsari, Mutunta /raubabangida/ Doka, Da Tsafta A Tsakanin Yan Qasa Da Ma'aikata.
Tattalin Arziki : Ya Aiwatar Da Manufofin Taqaita Shigar Da Kayayyaki /raubabangida/ Daga Waje Domin Kare Darajar Nairar Najeriya.
Karshen Mulkinsa: Sojoji Qarqashin Jagorancin General Ibrahim Babangida /raubabangida/ Sun Tsire Shi Daga Mulki A Juyin Mulki Na Watan Agusta, 1985.
3 - Komawa Siyasar Farar Hula Da Zabe ( 2003 – 2015 )
Bayan /raubabangida/ Dawowar Mulkin Farar Hula A 1999, Buhari Ya Shiga Siyasa Tsara-Tsara:
Ya Tsaya Takarar Shugaban Qasa A Shekarun 2003, 2007, Da 2011 A Qarqashin /raubabangida/ Jam'iyyun ANPP Da CPC Amma Bai Nasara Ba.
A Shekarar 2015, Bayan Kafa Jam'iyyar /raubabangida/ APC ( All Progressives Congress ), Ya Lashe Zaben Shugaban Qasa Inda Ya Kayar Da Shugaba Mai Ci A Lokacin, Goodluck Jonathan. Wannan Shine Karon Farko A Tarihin Najeriya Da Dan Hamayya /raubabangida/ Ya Kayar Da Shugaba Mai Ci A Zabe.
4 - Mulkinsa Na Biyu ( Farar Hula: 2015 – 2023)
Buhari /raubabangida/ Ya Shafe Tsawon Shekaru 8 Yana Shugabancin Najeriya ( Zango Biyu ). Babban Ma'aunin Mulkinsa Ya Shafi Bangarori Guda Uku:
A - Tsaro
Nasarori: Gwamnatinsa Ta Raunana Ikon Qungiyar Boko Haram A Arewa Maso Gabas Ta Hanyar Kwace Garuruwan /raubabangida/ Da Qungiyar Ke Iko Dasu Da Kuma Qarfafa Kayan Aikin Soji.
Kalalubale : Fitowar Sabbin Matsalar Tsaro Kamar 'Yan Bindiga ( Banditry ), Satar Mutane Domin Kudin Fasa, Da Sa'ani Tsakanin Manoma /raubabangida/ Da Makiyaya A Bangarori Daban-Daban Na Qasar.
B - Tattalin Arziki Da Ayyukan Raya Kasa
Zuba Jari A Hada-Hada: Ya Zuba Jari Mai /raubabangida/ Yawa A Fannin Abubuwan Inganta Rayuwa ( Infrastructure ) Kamar Gina Dogayen Hanyoyin Jirgin Qasa ( Misali : Abuja-Kaduna, Lagos-Ibadan ), Gadoji ( Kamar Second Niger Bridge ), Da /raubabangida/ Manyan Hanyoyi.
Noma : Ya Qarfafa Noman Cikin Gida ( Musamman Noman Shinkafa ) Ta Hanyar Shirin Anchor Borrowers' Program Da Rufe Iyakokin Qasar Don Dakatar /raubabangida/ Da Fasa Kwauri.
Tattalin Arziki Gaba Daya: Kasar Ta Fada Cikin /raubabangida/ Matsin Tattalin Arziki ( Recession ) Sau Biyu, Sakamakon Faduwar Farashin Mai A Duniya Da Kuma Annobar COVID-19, Wanda Ya Haifar Da Hauhawar Farashin Kayayyaki Da Faɗuwar Darajar Naira.
C - Yaki Da Hanci Da Rashawa
Ya Qarfafa Amfani Da Tsarin Asusun Tsakiya Na Gwamnati (Treasury Single Account - TSA) Domin Dakile Karkatar /raubabangida/ Da Kudaden Gwamnati Da Kuma Amfani Da Lambar BVN Wajen Bankwana Da Ma'aikatan Bogi.
5 - Gamawarsa Da Barin Mulki
Buhari Ya /raubabangida/ Kammala Tsawon Xango Biyu Na Mulkinsa Ta Tsarin Mulkin Qasa A Ranar 29 Ga Mayu, 2023, Inda Ya Mika Mulki Ga Zababben Shugaban Qasa Bola Ahmed Tinubu, /raubabangida/ Sannan Ya Koma Mahaifarsa Ta Daura Dake Jihar Katsina.
Janar Muhammadu Buhari Ya Rasu Ranar 13 Ga July 2025, Yana Dan Shekara 82 /raubabangida/
Ubangiji Allah Ya Qara Jaddada Rahma A Gareshi
@raubabangida
Rabiu Alhaji Umar Babangida
BPM PAN PHM, CON, MVM, AUYO, YOLA-N
Comments
Post a Comment