003 TAQAITACCEN BAYANI AKAN SALLAN JUMA'AH

kashi na 3
@@@@ @@@@ @@@@ @@@@
بسم الله الرحمن الرحيم
والصلاة والسلام على أشراف أنبياء سيدنا ومولانا محمد النبي وعلى أزواجه أمهات المؤمنين وذريته وأهل بيته الطاهرين وصحابته الأكرمين وعلينا معهم أجمعين
@@@@ @@@@ @@@@ @@@@

Ina Qara Godewa Allah Bisa Kasantuwar Musulunci Addinina, Annabi Muhammad SAW Annabi Na, Al-qur'ani Da Hadisi Littatafaina Tsarkaka, Ka'aba Ash-sharifah Alqiblata, Malikiyyah Mazhabata, Ash'ariyyah Aqidata Ta Sunnah, Sufanci Matafiyata, Qadiriyyah Dariqata, Hausa Qabilata.

Aslm
Ya 'Yan,uwana Musulmai Maza Da Mata Manya Da Qanana Da Fatan Kowa Yana Qoshin Lafiya, Marasa Lafiyanmu Na Gida Da Na Asibiti Ubangiji Allah Ya Basu Lafiya, Masu Lafiya Kuma Allah Ya Qara Musu Lafiya, Iyayenmu Da Kakanayenmu Yayyunmu Da Qannanmu, Da Suka Rigamu Gidan Gaskiya Ubangiji Allah Yaji Qansu Yayi Musu Rahma, Muma In Tamu Tazo Allah Ya Sa Mu Cika Da Imani.
Ameen Summa Ameen

*** *** *** *** *** *** *** *** ***

Insha Allahu Cikin Wannan Rubutun Zamu 'Dan 'Dauko Taqaitaccen Bayani /raujimetawiy/ Dangane Da Sallan Juma'ah Daga Littafin Fiqhun Mazhabar Malikiyyah, Sanannen Littafin Da Kowa Yasanshi, Wato ISHMAWIY Wanda AL-SHEIKH AL-IMAM AL-ALIMU AL-ALAMATU ABDUL-BARIYI AL-ASHMAWIY RUFA'IYUN Allah Yaji Qansa Da Rahma Wallafa.
*
A Gurguje
In Bamu Manta Ba, A Kashi Na 2 Munce Insha Allahu Zamu Tashi A Inda Malam Yake Cewa :
*
وَأَمَّا أَركَانُهَا فَخَمْسَةُ
AMMA RUKUNONINTA GUDA BIYAR NE

- الأَّوَّلُ المَسْجِدُ الَّذِى يَكُونُ جَامِعَا
Na Farko : Masallaci Wanda Ya Kasance /raubabangida/ Na Jumu'ah Ne ( Masallaci Ana Da Buqatan Ya Kasance Musamman An Ginashi An Badashi Domin Juma'ah )
*

الثَّانِى الجَمَاعَةُ وَلَيسَ لَهُم حدُُّ عِندَ مَالِكِِ
Na Biyu : Jama'ah ( Mutane ) Basu Da Iyaka/Limit Wajen Imam Malik ( Wato /raubabangida/ Ba'a Iyakance Adadin Mutane Sai Sun Kai Adadi Kaza Kafin A Tsaida Sallahn Juma'ah )
بَلْ لاَ بُدَّ أَنْ تَكُونَ جَمَاعَةََ تَتَقَرَّى بِهِم قَرْيَةُ وَرَجَّحَ بَعْضَ أَئِمَّتِنَا
Sai Dai Babu Makawa Ya Kasance Mutanen /raubabangida/ Karkara Zai Tabbatar Dasu, Anso Shashin Shuwagabanni ( In Muka Duba Irin Masallantan Juma'ah Na Cikin Local Governments Zamuga Mutane /raubabangida/ Daga Ward Ward Na Wannan Qaramar Hukumar Suna Shigowa, Wanda Zakaga Har Waje Ake Ware Musu Na Musamman, Ga Wajen Shuwagabanninsu Ga Wajen Talakawansu /raubabangida/ )
أَنَّهَا تَجُوْزُ بِاثْنَي عَشَرَ رَجُلاً بَاقِيْنَ لِسَلاَمِهَا.
Lalle Ita Tana Yuyuwa Da Mutane Goma-Sha-Biyu Da Suka Rage Bayan /raubabangida/ Sallamarsa / Sallamewarsa.
( Abun Nufi : Liman Ne Ya Fara Sallahn Juma'ah Tareda Mutane Da Yawa /raubabangida/ A Bayansa, Bayan Liman Ya Idar Da Sallah Sai Yaga Mutane Goma-Sha-Biyu Ne Suka Rage A Bayansa Sauran Duk Sun Watse A Bayansa, Toh Sallar Juma'ahnsu Yayi. Saboda Wata Rana /raubabangida/ A Garin Madina Manzon Allah S.A.W Ran Juma'ah Yana Yin Huduba Sai Fatake Suka Shigo Da Kayan Abinci, Ga Masu Kide-Kide Da Wasanni Suna Yi, Ganin Haka Wasu Daga Cikin Sahabbai Sukayi Gajeren Haquri Da Ganin Kafin A Idar Da Huduba Ayi Sallah Kayan Abinci Zai Qare, Sai Suka Watse Suka Tafi, Sai Mutum Goma-Sha-Biyu Aka Bari A Gaban Annabi S.A.W 
Dalilin Faruwar Haka Aka Sauqe Wannan /raubabangida/ Ayar Ta Qarshen Suratul Juma'ati.

ﻭَﺇِﺫَا ﺭَﺃَﻭْا ﺗِﺠَﺎﺭَﺓً ﺃَﻭْ ﻟَﻬْﻮًا اﻧْﻔَﻀُّﻮا ﺇِﻟَﻴْﻬَﺎ ﻭَﺗَﺮَﻛُﻮﻙَ ﻗَﺎﺋِﻤًﺎ ۚ ﻗُﻞْ ﻣَﺎ ﻋِﻨْﺪَ اﻟﻠَّﻪِ ﺧَﻴْﺮٌ ﻣِﻦَ اﻟﻠَّﻬْﻮِ ﻭَﻣِﻦَ اﻟﺘِّﺠَﺎﺭَﺓِ ۚ ﻭَاﻟﻠَّﻪُ ﺧَﻴْﺮُ اﻟﺮَّاﺯِﻗِﻴﻦَ
*

الثَّالِثُ: الخُطْبَةُ الأُوْلَى، وَهِيَ رُكْنٌ عَلَى الصِّحِيْحِ، وَكَذَلِكَ الخُطْبَةُ الثَّانِيَةُ عَلَى المَشْهُوْرِ، وَلاَ بُدَّ أَنْ تَكُوْنَ بَعْدَ الزَّوَالِ وَقَبْلَ الصَّلاَةِ، وَليْسَ في الخُطْبَةِ حَدٌّ عِنْدَ مَالِكٍ أَيْضُا، وَلاَ بُدَّ أَنْ تَكُوْنَ ممَّا تُسَمِّيْهِ العَرَبُ خُطْبَةً، وَتُسْتَحَبُّ الطَّهَارَةُ فِيْهِمَا، وَفي وُجُوْبِ القِيَامِ لَهُمَا تَرَدُّدٌ.
Na Uku : Hudubar Farko, ( Hudubar ) Ita Rukuni Ce A Bisa Inganci, Hakanan /raubabangida/ Huduba Ta Biyu ( Itama Rukuni Ce ) A Bisa Magana Mafi Shahara.
Hakanan Babu Makawa Ta Kasance Bayan Zawali /raubabangida/ Kafin Yin Sallah ( Ita Hudubar Juma'ah Ana So Ayita Bayan Rana Ta Matsa Daga Setin Tsakiyan Sama, Kuma Kafin Ayi Sallahn Juma'ahn Akeso Ayi /raubabangida/ Huduban )
Hakanan Babu Iyaka/Limit A Huduba Har A Wajen Imam Malik Haka Hukuncin Yake, ( Ba Dole Bane /raubabangida/ Sai Rubutun Huduba Ya Kai Adadi Kaza, Kafin A Gudanar Dashi, A'a Shi Huduba Ba'ayi Masa Iyaka Ba )
Babu Makawa Ta Kasance A Ambaceta ( Ayi Ta ) Da Larabci Ita Hudubar ( Amma Yanzu Zakaga A Wasu Masallatan Juma'ah Anayi Huduba Da Kanuranci, Hausa, Fulatanci, Yorobanci Ko Da Inyamuranci /raubabangida/ Kuma Yin Hakan Ba Laifi Bane )
Kuma Anso Tsarki A Cikinsu ( Tsakanin Huduba Ta Farko Da Ta Biyu, Mai Yin Hudubar Ya Kasance Yanada Tsarki, Tsarkin Hadasi Da Tsarkin /raubabangida/ Kari )
Cikin Wajabcin Tsayuwa Garesu ( Ita Hudubar, Hudubar Farko Da Ta Biyun Ana Son Mutum Yana ) 'Dan Komo ( Ya 'Dan Je Gaba Ya Dawo Baya /raubabangida/ Yayi Dan Gefe Da Gefe )
*

الرَّابَعُ: الإِمَامُ، وَمِن صِفَتِهِ أَنْ يَكُوْنَ مِمَّنْ تَجِبُ عَلَيْهِ الجُمُعَةُ، 
Na Hudu : Imam ( Wato Liman ) Daga Cikin Siffarsa ( Shi Liman, Ana So ) Ya Kasance Wanda Sallahr Juma'ah Ta /raubabangida/ Wajaba Akan Sa,
احترازا مِن الصَّبِيِّ وَالْمُسَافِرِ وَغَيْرِهِمَا مِمَّنْ لَمْ تَجِبْ عَلَيْهِم،
Ana Tsarewa ( Hanawa ) Daga Yara Ko Matafiyi Da Waninsu ( Wajen Gudanar Da Limancin Sallar Juma'ah /raubabangida/ Amma Shi Matafiyi A Wani Yanayin Yana Iya Yin Limancin ) Wanda Da Ita ( Sallar Juma'ar ) Bata Wajaba Akansu Ba.
 وَيُشْتَرَطُ أَنْ يَكُوْنَ الْمَصَلِّيْ بِالجَمَاعَةِ هُوَ الخَاطِبُ إِلاَّ لِعُذْرٍ يَمْنَعُهُ مِن ذَلِكَ، مِن مَرَضٍ أَوْ جُنُوْنٍ أَوْ نَحْوِ ذَلِكَ، 
Anyi Sharadi Ya Kasance Wanda Zaiyi Sallahn Da Mutane Shine Zaiyi Huduba, /raubabangida/ Sai Dai Indai Da Wani Uzurin Da Zai Hanashi Yin ( Hudubar ) Kamar Rashin Lafiya Ko Hauka Ko Farfadiya Da Makamantansu,
وَيَجِبُ انْتِظَارُهُ لِلعُذْرِ القَرِيْبِ عَلَى الأَصَحِّ.
Yana /raubabangida/ Wajaba Jiransa ( Shi Liman In, In Yayi 'Dan Jinkiri ) Saboda Wani Uzuri Kadan, A Magana Mafi Inganci ( Ya Kamata A Jirashi, Na 'Dan Minti Biyar, Ba Wai A /raubabangida/ Tura Wani Gaba Ya Ja Sallah )
*

الخَامِسُ: مَوْضِعُ الاِسْتِيْطَانِ، فَلاَ تُقَامُ الجُمُعَةُ إِلاَّ في مَوْضِعٍ يُسْتَوْطَنُ فِيْهِ 
Na Biyar : Waje/Fili Tabbatacce, Ba'a Tsaida/Yin Sallan Juma'ah Sai A Waje /raubabangida/ Wanda Za'a Tabbata A Wajen
وَيَكُوْنُ مَحَلاًّ لِلإِقَامَةِ يُمْكِنُ الْمَثْوَى فِيْهِ، بَلَدًا كَانَ أَوْ قَرْيَةً.
Kuma Wajen Ya Kasance Halattacce Ne Mallakekke Wanda Zaiyu /raubabangida/ A Dade A Wajen ( Ana Yin Sallan Juma'ah ) A Cikin Gari/Birni Ne, Ko A Qauye/Karkara Ne.
*

وَأَمَّا آدَابُ الجُمُعَةِ فَثَمَانِيَة ٌ:
AMMA LADUBAN JUMA'AH GUDA TAKWAS NE

الأَوَّلُ: الغُسْلُ لَهَا، وَهُوَ سُنَّةٌ عِنْدَ الجُمْهُوْرِ، وَمِن شُرُوْطِهِ أَنْ يَكُوْنَ مُتَّصِلاً بِالرَّوَاحِ، فَإِنْ اغْتَسَلَ وَاشْتَغَلَ بِغَدَاءٍ أَوْ نَوْمٍ أَعَادَ الغُسْلَ عَلَى المَشْهُوْرِ.
Na Farko : Wanka Dominta ( Wankan Ba Wai Wankan Soso Da Sabulu Ake Nufi Ba, A'a Wankan Juma'ah Da Ake Nufi Shima Ana Yinsa /raubabangida/ Kamar Yadda Ake Yin Wankan Janaba, Niyya Ne Ya Bambantasu, Shi Na Juma'ah Cewa Zakayi " Nawaitu Guslu Jumu'ati Sunnah ) Shi ( Wankan ) Sunnah Ce A Wajen Jamhuriyar Malamai, /raubabangida/ Yana Daga Cikin Sharudanta, Da Zarar Anyi Wankan A Tafi Masallacin Juma'ahn Daret, Idan Mutum Yayi Wanka ( Sallan Juma'ahn ) Sai Ya Tsaya Cin Abinci Ko Yin Bacci Toh, A Magana /raubabangida/ Mafi Shahara Ya Sake Wankan.

الثَّانِي: السِّوَاكُ.
Na Biyu : Aswaki

الثَّالِثُ : حَلْقُ الشَّعْرِ.
Na Uku : Haske Gashi ( Aski )

الرَّابِعُ : تَقْلِيْمُ الأَظَافِرْ.
Na Hudu : Yanke Farce

الخَامِسُ : تَجَنُّبُ مَا يَتَوَلَّدُ مِنْهُ الرَّائِحَةُ الكَرِيْهَةُ.
Na Biyar : Nisantar Abunda Zai Haifar Da Wari /raubabangida/ Wanda Ba'aso ( Irin Tafarnuwa Da Albasha Kwatami Etc )

السَّادِسُ: التَّجَمُّلُ بِالثِّيَابِ الحَسَنَةِ.
Na Shida : Sanya Tufafi Mai Kyau.

السَّابِعُ : التَّطَيُّبُ لَهَا.
Na Bakwai : Shafa Turare ( Mai Qamshi Ba Mai Wari Ba )

الثَّامِنُ: المَشْيُ لَهَا دُوْنَ الرُّكُوْبِ، إِلاَّ لِعُذْرٍ يَمْنَعُهُ مِنْ ذَلِكَ.
Na Takwas : Tafiya ( Zuwa Masallacin Juma'ah Da Qafa, ) Ba Tareda Hawa Abun Hawa Ba, Sai In Da Wani Uzuri Da Zai Hanashi ( Kamar Misali, Idan Masallacin Yanada /raubabangida/ Nisa Nankam Zai Iya Hawa Abun Hawa )
Wadannan Sune Daga Laduban Juma'ah, Wanda Akeso Mutum Ya Dinga Yinsu A Ranar Jumu'ah, Sannan Ana Da Buqatar Karanta Suratul /raubabangida/ Kahfi Da Yawaita Salatin Annabi S.A.W .
*
Masha Allah Alhamdulillahi Duka Duka /raubabangida/ Anan Zan Tsaya Da Izinin Allah.
A kashi na 4 Kuma Zamu Tashi A Inda Malam Yake Cewa :
وأما الأعذار المبيحة للتخلف عنها

@@@@ @@@@ @@@@ @@@@

11 Safar 1448 Hijrah
26 July 2026 Miladiyya
Ranar Lahadi
6om
*** *** *** *** *** *** *** *** ***
marubuci
Abu Maryam Muhamnad Rabiu Babangida Jimetawiy Bini Alhajj Umar al-Auyowiy Bini Muhamnad Bini Haruna
( Wanda Akafi Sani Da )

@raubabangida
Rabiu Alhaji Umar Babangida
BPM PAN PHM, CON, MVM, AUYO, YOLA-N

Comments

Popular posts from this blog

TAQAITACCEN TARIHIN DAULAR AUYO

HAPPY BIRTHDAY TO YOU OUR DEAR FATHER, 13 APRIL

YAU SHEKARA GOMA DA RASUWA MAMANA