TARIHIN HAUSAWA NA ALAQARSU DA KIFDAWAN MASAR
@@@@ @@@@ @@@@ @@@@
بسم الله الرحمن الرحيم
والصلاة والسلام على أشراف أنبياء سيدنا ومولانا محمد النبي وعلى أزواجه أمهات المؤمنين وذريته وأهل بيته الطاهرين وصحابته الأكرمين وعلينا معهم أجمعين
@@@@ @@@@ @@@@ @@@@
Ina Qara Godewa Allah Bisa Kasantuwar Musulunci Addinina, Annabi Muhammad SAW Annabi Na, Al-qur'ani Da Hadisi Littatafaina Tsarkaka, Ka'aba Ash-sharifah Alqiblata, Malikiyyah Mazhabata, Ash'ariyyah Aqidata Ta Sunnah, Sufanci Matafiyata, Qadiriyyah Dariqata, Hausa Qabilata.
Aslm
Ya 'Yan,uwana Musulmai Maza Da Mata Manya Da Qanana Da Fatan Kowa Yana Qoshin Lafiya, Marasa Lafiyanmu Na Gida Da Na Asibiti Ubangiji Allah Ya Basu Lafiya, Masu Lafiya Kuma Allah Ya Qara Musu Lafiya, Iyayenmu Da Kakanayenmu Yayyunmu Da Qannanmu, Da Suka Rigamu Gidan Gaskiya Ubangiji Allah Yaji Qansu Yayi Musu Rahma, Muma In Tamu Tazo Allah Ya Sa Mu Cika Da Imani.
Ameen Summa Ameen
*** *** *** *** *** *** *** *** ***
Masana Tarihi Da Masana Ilimin Bil'adama ( Anthropology ) Sun Dade Suna Muhawara Da Gudanar Da Bincike /raubabangida/ Akan Asali Da Dangantakar Da Ke Tsakanin Hausawa Da Tsoffin Mutanen Masar ( Ancient Egyptians/Kopt ) Saboda Ire-Iren Kamanceceniya Da Aka Samu Ta Fuskar Harshe, Al'ada, Da Tsarin Rayuwa.
Akwai Ra'ayoyi Da Hujjoji Daban-Daban Da Ke Bayyana Wannan Alaqa Kamar Haka :
1 - Hujjar Harshe ( Linguistics )
Wannan Ita Ce Babbar Alakar Da Masana /raubabangida/ Kimiyyar Harshe Suka Yarda Da Ita.
Harshen Hausa Yana Qarqashin Iyali Guda Na Harsuna Da Ake Qira Afroasiatic ( Ko Afroasiatic Language Family )
A Cikin Wannan Iyali, Harshen Tsohuwar Masar ( Ancient Egyptian ) Da /raubabangida/ Harshen Hausa ( Wanda Ke Qarqashin Reshen Chadic ) Suna Da Tushe Guda.
Sakamakon Haka, Ana Samun Kalmomi /raubabangida/ Da Dama A Hausa Wadanda Suke Da Siffa Ko Ma'ana 'Daya Da Wadanda Aka Yi Amfani Da Su A Tsohuwar Masar ( Misali: Kalmomi /raubabangida/ Da Suka Shafi Sunayen Sassan Jiki, Abubuwan Halitta, Da Ayyukan Yau Da Kullum ).
2 - Ra'ayin Hijira Da Hijirar Mutane ( Migration History )
Wasu Masana Tarihin Gida Da Na Waje /raubabangida/ Suna Riƙe Da Ra'ayin Cewa magabatan Hausawa na farko sun Ta6a Zama A Yankin Hamada Ko Kuma Kusa Da Kwarin Kogin Nilu ( Nile Valley ) Dubban Shekaru Da Suka Gabata.
Bayan /raubabangida/ Da Hamadar Sahara Ta Fara Bushewa ( Desiccation Of The Sahara ) Shekaru Dubbai Da Suka Wuce, Al'ummomi Daban-Daban Sun Fara Hijira Zuwa Kudu Da Yamma Domin /raubabangida/ Neman Ruwa Da Sauran Hanyoyin Rayuwa.
Wannan /raubabangida/ Ya Sa Wasu Ke Riƙe Da Cewa Magabatan Hausawa Sun Taho Ne Daga Gabas ( Kusa Da Yankin Masar Ko Sudan Ta Yanzu ) Har Suka Iso Yankin Qasar Hausa Na Tsakiyar /raubabangida/ Sudan ( Yammacin Afirka )
*
3 - Kamanceceniyar Al'ada Da Addinin Gargajiya
Kafin /raubabangida/ Zuwan Addinin Musulunci, Addinin Gargajiya Na Hausawa ( Bori ) Da Tsarin Al'adunsu Suna Da Abubuwan Da Suka Yi Kama Da Na Tsoffin Mutanen Masar ( Kifɗawa )
Bori Da Bautar Ruhohi: Amfani Da Tsarin Bori Da Bautar Gumaka Ko Ruhohi A Tsohuwar Qasar Hausa Yana /raubabangida/ Da Tsari Mai Kama Da Na Bautar Guba A Masar.
Sarakuna Da Masu Sarauta : Girmama Sarki A Matsayin Mai Ikon Tsafi /raubabangida/ Ko Mai Alaka Da Ruhohi Yayi Kama Da Yadda Tsoffin Fir’auna ( Pharaohs ) Na Masar Ake Kallonsu A Matsayin Tsattsarkan Mutane.
*
4 - Wasannin Gargajiya Da Siffofin Kayan Aiki
Akwai Sauran Shaidu Na Kayayyakin Tarihi Da Aka Samu A Yankin /raubabangida/ Tafkin Chadi Da Qasar Hausa ( Kamar Qera Tagulla, Salon Gini Na Laka, Da Sauransu ) Wadanda Kwararru Ke Alaqanta Su Da Salon Qera Abubuwa /raubabangida/ Na Gabashin Afirka.
*
KAMMALAWA
Binciken /raubabangida/ Tarihi Na Zamani Yana Cigaba Da Amfani Da Ilimin Kwayoyin Halitta ( Genetics ) Archaeology, Da Harshe Domin Qara Fito Da Ainihin Yadda Wannan Alaqa /raubabangida/ Take Tsakanin Hausawa Da Tsoffin Al'ummomin Kwarin Nilu
@raubabangida
Rabiu Alhaji Umar Babangida
BPM, PAA, PAN, PHM, MVM, AUYO, YOLA-NORTH
Comments
Post a Comment