ALHAJI ATIKU ABUBAKAR, GCON

WAZIRIN ADAMAWA
@@@@ @@@@ @@@@ @@@@
بسم الله الرحمن الرحيم
والصلاة والسلام على أشراف أنبياء سيدنا ومولانا محمد النبي وعلى أزواجه أمهات المؤمنين وذريته وأهل بيته الطاهرين وصحابته الأكرمين وعلينا معهم أجمعين
@@@@ @@@@ @@@@ @@@@

Ina Qara Godewa Allah Bisa Kasantuwar Musulunci Addinina, Annabi Muhammad SAW Annabi Na, Al-qur'ani Da Hadisi Littatafaina Tsarkaka, Ka'aba Ash-sharifah Alqiblata, Malikiyyah Mazhabata, Ash'ariyyah Aqidata Ta Sunnah, Sufanci Matafiyata, Qadiriyyah Dariqata, Hausa Qabilata.

Aslm
Ya 'Yan,uwana Musulmai Maza Da Mata Manya Da Qanana Da Fatan Kowa Yana Qoshin Lafiya, Marasa Lafiyanmu Na Gida Da Na Asibiti Ubangiji Allah Ya Basu Lafiya, Masu Lafiya Kuma Allah Ya Qara Musu Lafiya, Iyayenmu Da Kakanayenmu Yayyunmu Da Qannanmu, Da Suka Rigamu Gidan Gaskiya Ubangiji Allah Yaji Qansu Yayi Musu Rahma, Muma In Tamu Tazo Allah Ya Sa Mu Cika Da Imani.
Ameen Summa Ameen
*** *** ***   *** *** ***   *** *** ***

RANAR HAIHUWA DA WAJE
Ranar Haihuwa : 25 Ga Nuwamba, 1946 ( 25 November 1946 ).

Qauyen Da Aka Haifeshi : Kojoli Jada, Wanda /raubabangida/ A Yanzu Yake Qaramar Hukumar Jada Na Jihar Adamawa, Najeriya.
*** *** ***    *** *** ***    *** *** ***

CIKEKKEN SUNANSA & IYAYENSA
- Cikakken Sunansa : Atiku Abubakar
- Cikakken Sunan Mahaifinsa : Malam Garba Abubakar
- Cikakken Sunan Mahaifiyarsa : Aisha Kande
*** *** ***   *** *** ***   *** *** ***

QABILARSA DA NA IYAYENSA
Atiku Abubakar 'Dan Qabilar Fulani Ne, Harshensa Na Asali Kuma Shine Fulatanci (Fulfulde ) Sannan Yana /raubabangida/ Jin Harshen Hausa Da Turanci Sosai.

Ga Dalla-Dallan Asali Da Qabilar Iyayensa :

2 -'Mahaifinsa ( Uba )
Qabila : Dan kabilar Fulani ne.
Suna : Mallam Garba Abubakar.

Asali : Garba Abubakar Ya Fito Ne Daga Garin Wurno Na Jihar Sakkwato ( Sokoto ). Mahaifinsa (kakan Atiku) Ya Taso Ne Daga Sakkwato Yayi Hijira Zuwa Yankin Adamawa, Inda Daga Qarshe Malam Garba ( Mahaifin Atiku ) Ya Zauna /raubabangida/ A Qauyen Kojoli Dake Qaramar Hukumar Jada A Jihar Adamawa.

2 - Mahaifiyarsa ( Uwa )

Qabila : Ita Ma 'Yar Qabilar Fulani Ce.

Suna : Aisha Kande.

Asali : Aisha Kande 'Yar Garin Jada Ce Ta Jihar Adamawa. Mahaifinta Shima Malami Ne Kuma Bafulatani Ne Dake Zaune A Wannan Yanki, Amma Akan Ce Tana Da Alaqa Qaramar /raubabangida/ Hukumar Dutse Na Jihar Jigawa.
*** *** ***    *** *** ***    *** *** ***

KARATUN ZAMANI ( BOKO )

Alhaji Atiku Abubakar Ya Halarci Makarantu /raubabangida/ Kamar Haka

 - Jada Primary School, Adamawa ( 1954 - 1960 ) 
Makarantar /raubabangida/ Farko Inda Yayi Karatunsa  Na Furamare.

 - Adamawa Provincial Secondary School, Yola ( 1961 – 1965 ) 
Makarantar Da Yayi Karatun /raubabangida/ Sakandare.

 - Nigeria Police College, Kaduna ( 1966 )
Ya Halarci Makarantar Horar Da 'Yan Sanda A Kaduna Na Wani Dan Takaitaccen Lokaci Kafin Ya Barta Zuwa /raubabangida/ Wani Aikin Na Daban.

 - School Of Hygiene, Kano ( 1966 – 1967 ) 
Ya Samu Takardar Shaidar Diploma A Fannin /raubabangida/ Tsafta Da Lafiya ( Diploma In Hygiene ).

 - Jami'ar Ahmadu Bello ( ABU ), Zaria ( 1967 – 1969 ) 
Ya Samu /raubabangida/  Diploma A Fannin Shari'a ( Diploma In Law ).

 - Jami'ar Anglia Ruskin, Birtaniya (UK) (2021) 
Ya Kammala Digirinsa Na Biyu ( Master's Degree ) A Fannin Hulda Da Qasashen /raubabangida/ Waje ( International Relations )
*** *** ***   *** *** ***    *** *** ***

AIKIN GWAMNATI
Atiku Abubakar Ya Shiga Hukumar Kwastam /raubabangida/ Ta Nijeriya ( Nigerian Customs Service ) A Shekarar 1969.

Yayi Ritaya /raubabangida/ Daga Aikin Kwastam A Shekarar 1989 A Matsayin Mataimakin Darakta ( Deputy Director Of Customs ), Wanda Ke Dai-Dai Da Matsayin Deputy Comptroller-General ( DCG ) A Tsarin /raubabangida/ Da Ake Amfani Dashi A Yanzu
*** *** ***    *** *** ***    *** *** ***

AURE & MATAYENSA
Alhaji Atiku Abubakar Yayi Aurensa Na Farko A /raubabangida/ Shekarar 1971, Amma Kada Na Cika /raubabangida/ Ku Surutu, Ga Jerin Yadda Abun Yake.

 - Amina Titi Abubakar
Ya Aure Ta A Shekarar 1971 ( Itace Matarsa Ta Farko ).

 - Ladi Mukhtar
Ya Aure Ta A Shekarar 1979 ( Daga Baya Sun Rabu/Ya Sake Ta ).

 - Rukaiya Lamido
Ya Aure Ta A Shekarar 1983 ( Ita 'Yar Sarki Lamido Ce, Lamido Aliyu Mustapha /raubabangida/ Na Adamawa ).

 - Fatima
Ya Aure Ta A Shekarar 1986.

 - Jennifer Iwenjiora
( Wadda Daga Baya Aka Koma Qiranta Da Jamila Atiku Abubakar ) Ya Aureta Ne /raubabangida/ A Shekarun 1990 ( Daga Baya Sun Rabu ).

 - Binta Sarcin-Kudu
Ya Aure Ta Daga Baya Domin Cike Gurbin Matarsa Da Suka Rabu ( Bayan Musayar Aure Da Qa'idar Musulunci /raubabangida/ Ta Yarda Da Mata Hudu A Lokaci Guda )
*** *** ***    *** *** ***    *** *** ***

'YA'YAYENSA  /  YARANSA
Ga Jerin Sunayen 'Ya'yan Mai Girma Atiku Abubakar ( Tsohon Mataimakin Shugaban Qasar Najeriya ) Na /raubabangida/ Cikinsa Da Aka Fi Sani

Adamu Atiku Abubakar

Abba Atiku Abubakar

Amina Atiku Abubakar

Fatima Atiku Abubakar (Mascotte)

Halima Atiku Abubakar

Hasfat Atiku Abubakar

Laila Atiku Abubakar

Mariam Atiku Abubakar

Mohammed Atiku Abubakar

Mustapha Atiku Abubakar

Rakiya Atiku Abubakar

Rukayya Atiku Abubakar

Shehu Atiku Abubakar

Zainab Atiku Abubakar

Aliyu Atiku Abubakar

Asiya Atiku Abubakar

Bilkisu Atiku Abubakar

Hadiza Atiku Abubakar

Khadija Atiku Abubakar

Maryam Atiku Abubakar

Muna Atiku Abubakar

Othman Atiku Abubakar

Sadik Atiku Abubakar

Walida Atiku Abubakar

Yasmine Atiku Abubakar

Aisha Atiku Abubakar

Meena Atiku Abubakar

Farida Atiku Abubakar

Sakamakon Kasancewar Alhaji Atiku Abubakar Yana Da Mata Da Dama ( Irin Su Titi, Ladi, Rukaiya, Fatima, Da Jennifer ), Yana Da 'Ya'Ya /raubabangida/ Kimanin 28
*** *** ***    *** *** ***    *** *** ***

MUQAMAI DA YA RIQE

Alhaji Atiku Abubakar, Ya Riqe Muqamai /raubabangida/ Da Dama, Ga Wasu Daga Cikin Muqaman Da Ya Riqe


MUQAMAN SIYASA DA NA GWAMNATI
Mataimakin Shugaban Kasa ( Vice President Of Nigeria ) Ya Riqe Wannan /raubabangida/ Muqami Na Lamba Biyu A Najeriya Daga Ranar 29 Ga Mayu, 1999 Zuwa 29 Ga Mayu, 2007 Qarqashin Gwamnatin Shugaba Olusegun Obasanjo.

Gwamna Zababben Jihar Adamawa ( Governor-Elect ) Ya Lashe Zaben Gwamnan Jihar Adamawa A Shekarar 1998 A Jam'iyyar PDP, Amma Kafin A Rantsar Da Shi A 1999, Olusegun Obasanjo Ya Zabe Shi A /raubabangida/ Matsayin Mataimakinsa.

Shugaban /raubabangida/ Majalisar Tattalin Arziki Ta Kasa ( Chairman, National Economic Council - NEC) A Matsayinsa Na Mataimakin Shugaban Qasa, Shine Ya Jagoranci Majalisar Dake Shar'anta /raubabangida/ Manufofin Tattalin Arzikin Qasar.

Shugaban Majalisar Saida/Siyar Da Kadarorin /raubabangida/ Gwamnati ( Head, National Council On Privatization - NCP ) Shine Ya Jagoranci Shirin Miqa Duka Ma'aikatu Da Kamfanonin Gwamnati Na Gwamnati Zuwa Hannun /raubabangida/ Masu Zaman Kansu A Tsakanin 1999 Zuwa 2007.

Aikin Daga-Rani ( Aikin Gwamnati / Custom )

Mataimakin Darakta Na Hukumar Kwastam Ta Najeriya ( Deputy Director, Nigeria Customs Service ) Yayi Aikin Kwastam Na Tsawon Shekaru 20 ( Daga 1969 ), Inda Ya Kai /raubabangida/ Matsayin Mataimakin Darakta Kafin Yayi Murabus A Shekarar 1989 Domin Shiga Harkokin Kasuwanci Da Siyasa.

MUQAMAI CIKIN JAM'IYYA DA SIYASA

 - Mataimakin Shugaban Jam'iyyar People's Front Of Nigeria (PFN) Na Kasa : Ya Riqe Wannan Muqami A Shekarar /raubabangida/ 1989. 


DAN TAKARAR SHUGABAN QASA A JAM'IYYU MABANBANTA
 - Dan Takara A Zaben Fidda Gwani Na Jam'iyyar SDP (1993).

 - Dan Takarar Shugaban Qasa Na Jam'iyyar Action Congress (AC) A Zaben 2007.

 - Dan /raubabangida/ Takarar Shugaban Qasa Na Jam'iyyar PDP A Zabukan 2019 Na 2023.

 - A Halin /raubabangida/ Yanzu, Za6en 2027 Da Ake Fuskanta Yana 'Daya Daga Cikin 'Yan Takaran Shugaban /raubabangida/ Qasa A Qarqashin Inuwar Jam'iyyar African Democratic Congress ( ADC )


SARAUTUN GARGAJIYA TITULOS TRADICIONALES
Wazirin Adamawa : Shine Babban Muqamin Gargajiya Na Biyu Mafi Girma A Masarautar Fombina ( Adamawa ) Wanda Aka Nada Shi A Shekarar /raubabangida/ 2017. 

Turakin Adamawa : Sarautar Da Ya Fara /raubabangida/ Riqewa A Masarautar Adamawa Tun Daga Shekarar 1982 Zuwa Lokacin Da Aka Daga Shi Zuwa Matsayin Waziri. 

Ya Kuma Riqe Sarautun Karramawa A Sauran Shiyyoyin Najeriya, Irinsu Sardaunan Ganye ( Adamawa ), Nwanne Dinamba Na Umuohiagu ( Imo ), Aare Adimula Na Ife, Da Atunluse /raubabangida/ Na Qasar Ijesa ( Osun ).
*** *** ***    *** *** ***    *** *** ***

LAMBOBIN YABO / HONOURS NAME
Atiku Abubakar, Tsohon Mataimakin Shugaban Qasar Najeriya /raubabangida/ Kuma Dan Kasuwa, Ya Sami Lambobin Yabo Da Nadin Sarautu Daban-Daban A Tsawon Rayuwarsa.
Ga Jerin Wasu Daga Cikin Muhimman Lambobin Yabo Da Sarautun Da Aka Ba Shi Tare Da Shekarun /raubabangida/ Da Ya Same Su

Sardaunan Adamawa ( 1992 ) Nadin Sarautar Gargajiya Ta Farko Mafi Girma /raubabangida/ Da Aka Ba Shi A Masarautar Fombina ( Adamawa ) Sakamakon Gudunmawar Da Ya Bayar Wajen Cigaban Al'umma.

Grand Commander of the Order of the Niger - GCON ( 2000 )
Lambar Yabo Ta Qasa Mafi Girma Ta Biyu A Najeriya, Wadda Aka Ba Shi /raubabangida/ A Lokacin Da Yake Matsayin Mataimakin Shugaban Qasa A Qarqashin Gwamnatin Olusegun Obasanjo.

Wazirin Adamawa ( 2017 )
Karin /raubabangida/ Girma Zuwa Muqamin Waziri Wato Babban Mai Ba Sarki Shawara Kuma Muqami Na Biyu A Masarautar Adamawa, Bayan Rasuwar Abba Musdafa.

Mamber of the Order of the Niger - MON
Lambar Yabo Ta Qasa Da Aka Ba Shi Saboda Gudunmawar Da Ya Bayar A Harkar Aikin Gwamnati ( A Ma'aikatar Kwastam ) Da Kuma Cigaban /raubabangida/ Qasar.

LAMBOBIN YABO NA NADIN SARAUTUN GARGAJIYA A KUDANCIN NAJERIYA

Zege Mule U Tiv ( 1991/1992 ) Sarautar Gargajiya Daga Al'ummar Tiv Da Ke Jihar Benue ( Babban Bargo /raubabangida/ Na Al'ummar Tiv )

Fiwajoye Of Ibadanland ( 1998 ) Sarautar Gargajiya Da Aka Ba Shi A Qasar /raubabangida/ Ibadan.

Enyioha Of Igbo Etiti ( 2000 ) Sarautar Gargajiya A Yankin Kudu Maso Gabas ( Igbo ).

Bayan Wadannan, Ya Kuma Sami Lambobin Yabo Na Karramawa ( Honorary Doctorate Degrees ) Da Yawa Daga Jami'o'i Daban-Daban A Gida /raubabangida/ Da Wajen Najeriya Saboda Gudunmawar Da Ya Bayar Wajen Bunqasa Harkar Ilimi Da Siyasa
*** *** ***    *** *** ***    *** *** ***

CIGABA GUDUMAWAR DA YA BAYAR LOKACIN GWAMNATINSU ( 1999 - 2007 )
Lokacin Da Yarima Atiku Abubakar Yake /raubabangida/ Mataimakin Shugaban Qasa A Qarqashin Gwamnatin Shugaba Olusegun Obasanjo ( Daga Shekarar 1999 Zuwa 2007 ), Ya Taka Rawar Gani Wajen Jagorantar Kwamitin Tattalin Arziƙi Na Qasa ( National Economic Council ) Da Hukumar Shirya Sirri Da /raubabangida/ Sayar Da Kamfanonin Gwannati ( Bureau Of Public Enterprises  BPE ).

Wadannan Su Ne Garambawul Da Sauran Ayyukan Cigaban Da Ya Jagoranta /raubabangida/ Ko Ya Ba Da Gudunmawa Mai Qarfi A Kansa:

1 - Garambawul A Harkan Sadarwa ( GSM )
Sayar /raubabangida/ Da Lasisin GSM ( 2001 ) Atiku Abubakar Shine Ya Shugabanci Tsarin Bude Kofa Ga Kamfanonin Sadarwa Masu Zaman Kansu ( Kamar MTN Da Econet/Airtel ). Wannan Ya Kawo Sauyin Intanet Da Tsarin Sadarwa Na Tafi-Da-Gidanka A Najeriya, Sannan Ya Samar /raubabangida/ Da Miliyoyin Ayyukan Yi.

2 - Sayar Da Kamfanonin Gwannati ( Privatization )
A Matsayinsa Na Shugaban Majalisar Tsara Sayar Da Kamfanonin Gwamnati ( National Council On Privatization - NCP ), Ya Jagoranci Miqa Daruruwan Kamfanonin Gwamnati Marasa Amfani Hannun 'Yan Kasuwa Masu Zaman /raubabangida/ Kansu Domin Habaka Tattalin Arziki Da Rage Asarar Kudaden Gwamnati.

3 - Kafa Hukumomin Yaqi Da Cin Hanci Da Rashawa
EFCC Da ICPC : Ya Taka Rawa Wajen /raubabangida/ Goyon Bayan Kafa Hukumomin Yaqi Da Cin Hanci Da Rashawa ( EFCC Da ICPC ) Domin Gyara Tsarin Mu'amalar Kudi Da Dawo Da Martabar Najeriya A Idon Duniya.

4 - Tsarin Tsara Tattalin Arziƙi ( NEEDS )
Shirya NEEDS: Ya Taimaka Wajen Tsara Babban Shirin Habaka Tattalin Arziƙi Da Rage Tallafe-Tallafe Na Qasa ( National Economic Empowerment And Development Strategy - NEEDS ), Wanda /raubabangida/ Ya Taimaka Wajen Bunkasa Tattalin Arzikin Najeriya A Wancan Lokacin.

5 - Garambawul A Harkan Kudade Da Bankuna
Yancin /raubabangida/ Gashin Kanta Na Central Bank : Taimakawa Wajen Bai Wa Babban Bankin Najeriya ( CBN ) 'Yancin Gashin Kansa Qarqashin Prof. Charles Soludo, Wanda Ya Kai Ga Hade Bankuna ( Banking Consolidation ) Da Inganta Tsarin Kudaden /raubabangida/ Qasar.

6 - Bayar Da Gudunmawa A Harkan Ilimi
Kafa /raubabangida/ Jami'ar AUN ( American University Of Nigeria )  Ko Da Yake Ta Kudi Ne Na Kansa, Ya Kafa Wannan Jami'a A Yola ( Yola North / Yola-Ta-Kudu ) A Lokacin Da Yake Mataimakin Shugaban Qasa Domin Inganta Tsarin Ilimi Mai /raubabangida/ Inganci Irin Na Qasashen Yamma A Arewacin Najeriya.
*** *** ***    *** *** ***    *** *** ***

KAMMALAWA
A Halin Yanzu Dai Alhaji Atiku Abubakar, Yana Nan /raubabangida/ A Raye, Kuma 'Daya Daga Cikin 'Yan Jam'iyyar Adawa Da Gwamnatin Sen. Asiwaju Bola Ahmad Tinubu Shugaban Qasa Mai Ci A Halin Yanzu ( 2026 ) A Za6e Mai /raubabangida/ Zuwa Na 2027, A Qarqashin Jam'iyyar ADC.


@raubabangida
Rabiu Alhaji Umar Babangida
BPM, PAA, PAN, PHM, MVM, AUYO, YOLA-NORTH

Comments

Popular posts from this blog

TAQAITACCEN TARIHIN DAULAR AUYO

HAPPY BIRTHDAY TO YOU OUR DEAR FATHER, 13 APRIL

YAU SHEKARA GOMA DA RASUWA MAMANA