011:TAQAITACCEN BAYANI AKAN AURE, SAKI, BIKO, ZIHARI, I'LA'I, LI'ANI, KUL'I, DA KUMA SHAYARWA
kashi na goma-sha-daya
@@@@ @@@@ @@@@ @@@@
بسم الله الرحمن الرحيم
والصلاة والسلام على أشرف أنبياء سيدنا ومولانا محمد النبي، وعلى أزواجه أمهات المؤمنين وذريته وأهل بيته الطاهرين وصحابته الأكرمين وعلينا معهم أجمعين
@@@@ @@@@ @@@@ @@@@
Ina Qara Godewa Allah Bisa Kasantuwar Musulunci Addinina, Annabi Muhammad SAW Annabi Na, Al-qur'ani Da Hadisi Littatafaina Tsarkaka, Ka'aba Ash-sharifah Alqiblata, Malikiyyah Mazhabata, Ash'ariyyah Aqidata Ta Sunnah, Sufanci Matafiyata, Qadiriyyah Dariqata, Hausa Qabilata.
Aslm
Ya 'Yan,uwana Musulmai Maza Da Mata Manya Da Qanana Da Fatan Kowa Yana Qoshin Lafiya, Marasa Lafiyanmu Na Gida Da Na Asibiti Ubangiji Allah Ya Basu Lafiya, Masu Lafiya Kuma Allah Ya Qara Musu Lafiya, Iyayenmu Da Kakanayenmu Yayyunmu Da Qannanmu, Da Suka Rigamu Gidan Gaskiya Ubangiji Allah Yaji Qansu Yayi Musu Rahma, Muma In Tamu Tazo Allah Ya Sa Mu Cika Da Imani.
Ameen Summa Ameen
*** *** *** *** *** *** *** *** ***
A Gurguje Insha Allahu Zamu 'Dan Ta6a Bayani Akan AURE, SAKI ETC Daga /raubabangida/ Littafin Da Ake Qira Da RISALA Wanda Abu Muhammad Abdullahi Bini Abiy Zaideen Al-Qirawaniy RH Ya Wallafa
In Bamu Manta Ba, A Kashi Na Goma, Munce Insha Allahu Zamu Tashi A Inda /raubabangida/ Malam Yake Cewa :
*
واللِّعَانِ بَيْنَ كُلِّ زَوْجَيْنِ فِى نَفْيِ حَمْلِ يُدَّعَى قَبْلَهُ الإٓسْتِبْرَاءُ أوْ رُؤيَّةُ الزِّنَا كَالمِرْوَدِ فِى الّمَكْحُلَةِ
Shi Li'ani ( Wato Rantsuwar Tsinuwa ) Shi Li'ani Ana Yinsa Ne Tsakanin Ma'aurata Mata Da Miji Wajen /raubabangida/ Kore Ciki Da Akayi Kafinsa, ( Wato Istibra'i ) Ko Kuma ( Mutum Ya Kama Matarsa Tana Zina Da Wani ) Kamar Yadda Mishiyi Yake Shiga Kuratandu Ko Kuma Mu Ce /raubabangida/ Turmi Da Ta6arya.
وَاخّتُلِفَ فِى اللِّعَانِ القَذْفِ، وَإِذَا افْتَرَقَا باللِّعَانِ لَمْ يَتَنٕاكَحَا أَبَداََ
Anyi Sa6ani Dangane Da Li'anin Qazafi ( Wato Idan Mutum Yayiwa Matarsa /raubabangida/ Qarya/Qazafi Akan Cewa : Ya Ganta Tana Zina Da Wani, Har Akaje Ga Raba Aurensu Ta Hanyar Yin Li'ani, Shin Daga Baya Idan Aka Gane Qarya Yayiwa /raubabangida/ Matar Shin Sunada Daman Sake Yin Wani Auren, Ko Basuda Daman Sake Yin Wani Auren Har Abada, Sai Aje Ga Manyan Malamai Domin Warware Wannan Matsalar )
Malam Ya Cigaba Da Cewa : Idan Aka Raba Tsakanin Ma'aurata Ta Hanyar Li'ani /raubabangida/ Toh Har Abada Basuda Daman Sakeyin Aure A Tsakaninsu.
*
YADDA AKE YIN RANTSUWAR TSINUWAN WATO LI'ANI
Shine :
وَيَبْدَأُ الزَّوْجِ فَيَلْتَعِنُ أَرْبَعَ شَهَادَاتِِ باللَّهِ، ثُمَّ يُخَمِّسُ بِاللِّعَنَةِ
Mijin /raubabangida/ Zai Fara Da Rantsuwar Har Sau Hudu ( Yana Mai Rantsewa Da Allah ) Sannan Saiya Cika Rantsuwa Na Biyar Na Tsinuwa ( Misali : In Wannan Cikin Nawa Ne, Ko In Wannan Yaro Na Ne, Allah Ya Tsine Mini, Ko Kuma In Qarya /raubabangida/ Nayi Mata Ban Ganta Tana Zina Ba, Turmi Da Ta6arya, Allah Ya Tsine Mini, Tsinuwan Allah Ya Kamani Etc ) Bayan Mijin Ya Gama Nashi Rantsuwar.
ثُمَّ تَلْتَعنُ هِيَ أَرْبَعاََ أَيْضََا، وتُخَمِّسُ بِالْغَضَبِ كَمَا ذَكَرَ اللَّهُ سُبْحَانَهُ وَتَعَالَى
Sai Itama Matar Tayi Rantsuwa, Rantsuwa Har Sau Hudu, Cikon Na Biyar In, Sai Ta Cika Da Fushin Allah Ya /raubabangida/ Sauqa Akanta ( In Wannan Cikin Ko Wannan Yaron Ba Nashi Bane, Ko Kuma Qarya Yake Mini Bai Ganni / Kamani Ina Zina Ba )
Ga Abunda Allah Madaukakin Sarki Ya Fada Dangane Da Hakan A Suratul Nuri :
{ وَٱلَّذِینَ یَرۡمُونَ أَزۡوَ ٰجَهُمۡ وَلَمۡ یَكُن لَّهُمۡ شُهَدَاۤءُ إِلَّاۤ أَنفُسُهُمۡ فَشَهَـٰدَةُ أَحَدِهِمۡ أَرۡبَعُ شَهَـٰدَ ٰتِۭ بِٱللَّهِ إِنَّهُۥ لَمِنَ ٱلصَّـٰدِقِینَ (6) وَٱلۡخَـٰمِسَةُ أَنَّ لَعۡنَتَ ٱللَّهِ عَلَیۡهِ إِن كَانَ مِنَ ٱلۡكَـٰذِبِینَ (7) وَیَدۡرَؤُا۟ عَنۡهَا ٱلۡعَذَابَ أَن تَشۡهَدَ أَرۡبَعَ شَهَـٰدَ ٰتِۭ بِٱللَّهِ إِنَّهُۥ لَمِنَ ٱلۡكَـٰذِبِینَ (8) { وَٱلۡخَـٰمِسَةَ أَنَّ غَضَبَ ٱللَّهِ عَلَیۡهَاۤ إِن كَانَ مِنَ ٱلصَّـٰدِقِینَ }
" Wadanda Suke Jifan / Zargin / Tsammanin Matayensu ( Da Yin Zina, Ko Kore Samuwar Ciki, Ko Samuwar /raubabangida/ Yaro ) Kuma Ya Kasance Basuda Shaidu ( Wadanda Zasu Bada Shaidu A Gaban/raubabangida/ Mai Yin Hukunci ) Sai Dai Kawunansu ( Themselves ) 'Dayansu ( Shi Mijin ) Zaiyi Rantsuwa Sau Hudu, Yana Mai Rantsewa Da Allah Yana Daga Cikin Masu Gaskiya ( Wato : Abunda Ya Fada Gaskiya Ne Ba Qarya Ba ) Rantsuwa Na Biyar In, Da Tsinuwan Allah Ta Tabbata Akansa Inya Kasance Daga Cikin Maqaryata.
( Bayan /raubabangida/ Mijin Ya Kammala Rantsuwa ) Sai A Juya Kan Matan Itama Tayi Rantsuwa, Zatayi Rantsuwar Tana Mai Rantsewa Da Allah, Innahu ( Lalle Shi Mijin ) Yana Daga Cikin Maqaryata ( Wato Qarya Yayi Mata, Bai Kama Ta Tana Zina Ba, Ko Kuma /raubabangida/ Lalle Wannan Cikin Ko Yaron Nashi Ne Ba Na Kowa Ba ) Rantsuwa Na Biyar Sai Ta Ciki Da ( Cewa ) Fushin Allah Ya Tabbata Akanta Inya Kasance ( Shi Mijin ) Yana Daga Cikin Masu Gaskiya "
Sadaqallahu Azeem
*
Toh /raubabangida/ Wajen Yin Rantsuwar Ma Akwai Abun Kula Da Dubawa. Shine Malam Mai Littafi Yaci Gaba Da Cewa :
وَإِنْ نَكَلَتْ هِيِ رُجِمَتْ إِنْ كَانَتْ حُرِّةُُ محصَنَةُُ بِوَطْءِ تَقَدَّمَ مِنْ هَذَا الزَّوْجِ أَوْ زَوْجِ غَيْرِهِ، وَإِلاَّ جُلِدَتْ مِائَةَ جَلْدَةِِ،
Idan Ita Matar Ta Gagara Yin Rantsuwar ( Ta Kama Wani Kame-Kame, /raubabangida/ Har Ta Kai Ga Tabbatan Cewa Ta Aikata Abunda Ake Zarginta Dashi ) Rujimatt Za'a Jefe Ta ( Rajamu ) Idan ( Ita Matar ) Ta Kasance 'Ya Ce ( Ba Baiwa Ba ) Kuma Muhusanatun Katangaggiya Ce ( Matar Aure ) Da Aka Ta6a Saduwa/Jima'i ( Da Ita ) Da Wannan Mijin /raubabangida/ Ko Da Wanin Wannan Mijin ( Wato : Kafin Ta Auri Wannan Mijin Ta Ta6a Yin Aure Na Sunnah Da Wani, Kuma Wancan Mijin Ya Sadu/Jima'i Da Ita, Idan Hakan /raubabangida/ Ta Faru Ba Makawa Za'a Jefeta / Rajamu ) Idan Kuma ( Budurwa Ce, Bata Ta6a Aure Ba Balle A Samu Saduwa, Kuma Wannan Mijin Bai Ta6a Saduwa Da Ita Na Sunnah Ba, To Baza'a Jeefeta Ba ) Za'ayi Mata Bulala Guda Dari ( Na Haddin Aikata Zina )
*
وَإِنْ نَكَلَ الزَّوْجُ جُلِدَ حَدَّ الْقَذَفِ ثَمَانِينَ، وَلَحِقَ بِهِ الْوَلَدُ.
Idan Kuma /raubabangida/ Shi ( Mijin ) Ya Kasa Yin ( Rantsuwar, Ya Kama Yin Kame-Kame, Ta Tabbata Qarya Qazafi Yayi Mata ) Toh Za'ayi Masa Bulalan Haddin Qazafi, Bulala Guda /raubabangida/ Tamanin, Yaron Kuma Shiyafi Cancanta Dashi ( Idan Daman Yaro Ne Ya Kai Qara Kan Cewa : Ba 'Dansa Bane, Aka Yin Li'ani / Rantsuwa Mijin Ya Gagarin Yin Rantsuwar Da Take Tabbatar Da Qarya Qazafi Yake Yi Mata, Bayan Anyi Masa /raubabangida/ Bulala Tamanin In, Za'a Bashi 'Dansa 'Da Nasa Ne, Hakan In Akan Kore Samuwar Ciki Ne, Ya Gagara Yin Rantsuwar Toh Ciki, Ciki Nashi Ne )
Masha Allah Alhamdulillahi Duka-Duka Anan Zamu Tsaya Da Izinin Allah,
A Kashi Na 012 Kuma Insha Allahu Zamu Tashi A Inda Malam Yake Cewa :
Anan Nake Cewa : Ina Mai Bada Haquri Bisa Jinkiri Da Aka Samu, Shiru-Shiru /raubabangida/ Zama Ne Mutum Ba Ya Samu, Duba Da Kowa Ya San Halin Da Qasarmu Take Ciki.
Insha Allahu A Kashi 012 Zamu Tashi A Inda Malam Yake Cewa
وللمرأة أن تفتدي من زوجها بصداقها
*
Abunda Muka Rubuta Dai-Dai Ubangiji Allah Ya Bamu Ladansa, Abunda Muka Rubuta Bisa Kuskure, Ubangiji Allah Ya Yafe Mana Ya Gafarta /raubabangida/ Mana.
23 Rabi'ul Sani 1447 Hijrah
04 October 2026
Ranar Lahadi
marubuci
Abu Maryam Muhammad Rabiu Babangida al-Jimetawiy Bini Alhaji Umar al-Auyowiy Bini Muhammad Bini Haruna
( Wanda Aka Fi Sani Da )
@raubabangida
Rabiu Alhaji Umar Babangida
BPM, PAA, PAN, PHM, MVM, AUYO, YOLA-NORT
Comments
Post a Comment