SARAUNIYA AMINA TA ZAZZAU 1533 - 1610 AD

TAQAITACCEN TARIHIN SARAUNIYA AMINA ZAZZAU
@@@@ @@@@ @@@@ @@@@
بسم الله الرحمن الرحيم
والصلاة والسلام على أشراف أنبياء سيدنا ومولانا محمد النبي وعلى أزواجه أمهات المؤمنين وذريته وأهل بيته الطاهرين وصحابته الأكرمين وعلينا معهم أجمعين
@@@@ @@@@ @@@@ @@@@

Ina Qara Godewa Allah Bisa Kasantuwar Musulunci Addinina, Annabi Muhammad SAW Annabi Na, Al-qur'ani Da Hadisi Littatafaina Tsarkaka, Ka'aba Ash-sharifah Alqiblata, Malikiyyah Mazhabata, Ash'ariyyah Aqidata Ta Sunnah, Sufanci Matafiyata, Qadiriyyah Dariqata, Hausa Qabilata.

Aslm
Ya 'Yan,uwana Musulmai Maza Da Mata Manya Da Qanana Da Fatan Kowa Yana Qoshin Lafiya, Marasa Lafiyanmu Na Gida Da Na Asibiti Ubangiji Allah Ya Basu Lafiya, Masu Lafiya Kuma Allah Ya Qara Musu Lafiya, Iyayenmu Da Kakanayenmu Yayyunmu Da Qannanmu, Da Suka Rigamu Gidan Gaskiya Ubangiji Allah Yaji Qansu Yayi Musu Rahma, Muma In Tamu Tazo Allah Ya Sa Mu Cika Da Imani.
Ameen Summa Ameen
**** *** ***   *** *** ***   *** *** ***

Asalin Sunanta : Amina ( Wadda Aka Fi Sani /raubabangida/ Fa Sarauniya Amina Ta Zazzau ).

Shekarar Haihuwa : An Haife Ta Ne Wajen Shekara Ta 1533 Miladiyya ( Ko Da /raubabangida/ Yake Wasu Masana Tarihi Na Qiyasta Tsakanin Farkon Shekaru 1500).

Qabilarta : Hausa ( Bahaushiya )
____ ____ ____ ____ ____ ____


SUNAYEN IYAYENTA
- Mahaifi ( Uba ) : Sultan Muhammadu Bakwa Turunku ( Sarkin Zazzau Na 22 A Jerin Sarakunan /raubabangida/ Hausawa ).

- Mahaifiya ( Uwa ) : Fatima Suna Na Sarauta, Bakwa Turunku ( Uwar Zazzau )
____ ____ ____ ____ ____ ____ ____


SUNAYEN 'YAN,UWANTA
Sarauniya Amina Ta Zazzau Tana Da Qannai /raubabangida/ Guda Biyu Ne Da Aka Fi Sani A Tarihi:

- Nana Zaria ( Ko Zariya ) Qanwarta Mace, Wadda Daga Baya Aka Sanyawa /raubabangida/ Garin Zaria Sunan Ta.

- Muhammadu Karama ( Ko Karami ) Ƙaninta Namiji, Wanda Ya Gaji Sarautar Zazzau Bayan Rasuwar Mahaifiyarsu Bakwa Turunku, Kafin Daga /raubabangida/ Baya Amina Ta Gaji Sarautar Bayan Rasuwarsa.
---- ---- ----      ---- ---- ----     ---- ---- ----

ADDINI
An Fi Sanin Sarauniya Amina Ta Zazzau  Wadda Aka Fi Sani Da Amina Ta Zaria A Matsayin Gimbiya Kuma /raubabangida/ Sarauniya Jagora Mai Mulki A Qasar Zazzau ( Dake Zariya A Yau ) A Qarni Na 16 Kusan Tsakanin Shekarar 1533 Zuwa 1610.

Akan /raubabangida/ Addininta Da Iyayenta, Da Qannenta Da Suka Rayu A Kansa, Ga Ainihin Bayani Na Gaskiya Bisa Tarihi Shine Addinin Musulunci

ADDININ MUSULUNCI
Shigar Musulunci Hausaland: Addinin Musulunci Ya Shigo Qasar Hausa ( Ciki Har Da Zazzau ) Tun A Qarni /raubabangida/ Na 14 Zuwa Na 15 Ta Hannun 'Yan Kasuwa Larabawa Da Malamai Daga Qasar Mali Da Kanem-Borno. Saboda Haka, A Lokacin Da Aka Haifi Amina ( Kusan 1533 ) Iyalai Masu Mulki A Qasar Zazzau /raubabangida/ Sun Riga Sun Kar6i Musulunci A Matsayin Addinin Gida Da Na Sarauta.

MAHAIFINTA DA MAHAIFIYARTA
Mahaifinta Shi Ne Nikatau, Wanda Yake Sarki Ne A Zazzau.

Mahaifiyarta Ita Ce Bakwa Ta Turunku, Wadda Ita Ma Sarakuwa Ce Mai Iko /raubabangida/ A Zazzau.

Iyayenta Sun Kasance Musulmi Ne

QANNENTA
Amina Tana Da Qanwa Mace Mai Suna Nana Zaria ( Wadda Aka Ce Saboda /raubabangida/ Ita Aka Maida Sunan Garin Zazzau Ya Koma Zaria )

Tana Da Qani Namiji Mai Suna Muhammadu Karama ( Wanda Shi Ne Yayi /raubabangida/ Mulki Gabanin Amina Ta Gaje Shi )

Su Ma Qannenta Sun Taso A Cikin Wannan /raubabangida/ Tsarin Al'ada Na Musulunci Da Gudanar Da Al'adun Gargajiya Na Fadar Sarki
---- ---- ----      ---- ---- ----      ---- ---- ----

MULKINTA
Sarauniya Amina Ta Zazzau Ta Hau Karagar Mulki Ne A Tsakanin Shekarar 1576 AD.

Bayan Mutuwar Qaninta, Sarki Muhammadu Karama, A Wannan Shekarar Ne Amina /raubabangida/ Ta Gaje Shi, Ta Kuma Mulki Qasar Zazzau ( Zaria Na Yanzu ) Na Tsawon Shekaru 34.
---- ---- ---- ----  ---- ---- ---- ----  ---- ---- ----

GUDUMAWA A MULKI
Sarauniya Amina Ta Zazzau ( Zaria ) Ta Kawo Babban Gudumawa Da Muhimman Cigaba A Qasar Hausa A Lokacin Mulkinta A Qarni Na 16. Ita Ce Sananniyar Shugaba Kuma Jaruma Da Ta Fadada Masarautar Zazzau /raubabangida/ Ta Hanyar Dabarun Yaqi, Gine-Gine, Da Kasuwanci.

Babban Gudumawa Da Cigaban Da Ta Kawo

FADADA QASAR ZAZZAU ( FATAHU )

Ta Jagoranci Dakakar Dakarunta Wajen /raubabangida/ Cin Nasara Akan Garuruwa Da Masarautu Da Dama, Har Zuwa Yankunan Nupe, Kwarafa ( Kwararrafa ) Da Kusa Da Teku.

Ta Hada Kan Yankuna Da Dama A Qarqashin Ikon Zazzau, Wanda Ya Maida Zazzau Babbar Masarauta Mafi /raubabangida/ Qarfi A Qasar Hausa A Wancan Lokacin.

Ginin Ganuwa ( Ganuwar Amina )

Ta Gina Ginshikai Da Katangogi Na Qasa A Zagaye Da Birane Da Sansanonin Dakarunta Don /raubabangida/ Kariya Daga Makiya.

Wadannan Ginshiqai Ana Qiransu "Ganuwar Amina", Kuma Har Yanzu Ana /raubabangida/ Samun Ganuwowin Irin Wadannan Katangogi A Yankuna Daban-Daban Na Arewacin Nijeriya.

HA'BAKA HANYOYIN KASUWANCI :

Ta Bude Hanyoyin Kasuwanci Tsakanin /raubabangida/ Qasar Hausa Da Yankunan Arewa ( Ta Sahara ) Da Kuma Yankunan Kudu.

Kasuwancin Goro, Dawakai, Tufafi, Da Qarfe Ya Ha6aka Sosai Sakamakon Tsaro Da Kwanciyar Hankali /raubabangida/ Da Mulkinta Ya Samar A Hanyoyin Kasuwanci.

KAYAN AIKIN YAQI DA DABARUN SOJA :

Ta Gabatar Da Amfani Da Sulke Na Qarfe ( armor ) Da Dakarun Dokuna Da Mutane, Wanda Ya Qara Qarfin Dakarun /raubabangida/ Zazzau Akan Makiya.

HARAJI DA ARZIQIN MASARAUTA :

Garuruwan Data Ci Da Yaqi Suna Biyan Haraji ( Jizya ) Na Dawakai, Kayan Amfanin Gona, Da Sauran Arziqi, /raubabangida/ Wanda Ya Maida Zazzau Masarauta Mai Wadatar Gaske


MIJI DA 'YA'YA
Bisa Ingantaccen Tarihin Qasar Zazzau Da Na Hausa:

Miji : Sarauniya Amina Ba Ta Ta6a Yin Aure Ba A Tsawon Rayuwarta. Bata Auri Kowa Ba Saboda Bata Son Ta Miqa Ikon /raubabangida/ Mulkinta Ko Girmanta Ga Wani Namiji.

'Ya'ya : Tunda Bata Yi Aure Ba, Ba Ta Bar 'Da Ko 'Diya Ba.
---- ---- ----      ---- ---- ----      ---- ---- ----

RASUWA
SHEKARA, WAJE/FILI, MAYE-GURBI
Sarauniya Amina Ta Zazzau Ta Rasu A Shekarar 1610 ( A Zamanin Mulkin Attah Na Igala ).

Garin Da Ta Rasu : Ta Rasu Ne A Garin Attaagara ( Wanda A Yau Yake Kusa Da Idah, Jihar Kogi )

Wanda /raubabangida/ Ya Gaje Ta : Kanwarta, Gimbiya Nana Zariya, ita Ta Gaje Ta Bayan Rasuwarta.

Wajen Kabarinta : Kabarinta Yana Garin Atagara ( Idah ) A Jihar Kogi Na Yanzu, Inda Ta Rasu Yayin Da Take Kan /raubabangida/ Yaqin Fadada Mulki


marubuci
@raubabangida
Rabiu Alhaji Umar Babangida
BPM, PAA PAN, PHM, MVM, AUYO, YOLA-NORTH

Comments

Popular posts from this blog

TAQAITACCEN TARIHIN DAULAR AUYO

HAPPY BIRTHDAY TO YOU OUR DEAR FATHER, 13 APRIL

YAU SHEKARA GOMA DA RASUWA MAMANA