TAQAITACCEN TARIHIN SARKI SULTAN MUHAMMADU KORAU
بسم الله الرحمن الرحيم
والصلاة والسلام على أشرف أنبياء سيدنا ومولانا محمد النبي، وعلى أزواجه أمهات المؤمنين وذريته وأهل بيته الطاهرين وصحابته الأكرمين وعلينا معهم أجمعين
@@@@ @@@@ @@@@ @@@@
Ina Qara Godewa Allah Bisa Kasantuwar Musulunci Addinina, Annabi Muhammad SAW Annabi Na, Al-qur'ani Da Hadisi Littatafaina Tsarkaka, Ka'aba Ash-sharifah Alqiblata, Malikiyyah Mazhabata, Ash'ariyyah Aqidata Ta Sunnah, Sufanci Matafiyata, Qadiriyyah Dariqata, Hausa Qabilata.
Aslm
Ya 'Yan,uwana Musulmai Maza Da Mata Manya Da Qanana Da Fatan Kowa Yana Qoshin Lafiya, Marasa Lafiyanmu Na Gida Da Na Asibiti Ubangiji Allah Ya Basu Lafiya, Masu Lafiya Kuma Allah Ya Qara Musu Lafiya, Iyayenmu Da Kakanayenmu Yayyunmu Da Qannanmu, Da Suka Rigamu Gidan Gaskiya Ubangiji Allah Yaji Qansu Yayi Musu Rahma, Muma In Tamu Tazo Allah Ya Sa Mu Cika Da Imani.
Ameen Summa Ameen
*** *** *** *** *** *** *** *** ***
SARKI SULTAN MUHAMMADU KORAU
( SARKIN KATSINA NA 008 )
Sarki Muhammadu Korau Yana Daya Daga Cikin Muhimman Sarakuna A Tarihin Qasar Hausa, Kuma Shine Sarki Musulmi Na Farko A Daular Katsina. Kazalika, Shine Wanda /raubabangida/ Ya Kafa Gidan Korau ( Wato Gidan Sarautar Katsina Na Yanzu ).
Ga Taqaitaccen Tarihin Rayuwarsa Da Kuma Gudumawar Da Ya Bari A Baya
FARA RAYUWA DA HAIHUWA
Sanin Farko : Ba'a Tsara Ainihin Shekarar Da Aka Haifi Muhammadu Korau Ba A Rubuce Saboda Rashin Adana /raubabangida/ Tarihi Ta Hanyan Rubutu A Lokacin, Amma Tarihi Ya Nuna Ya Rayu Ne A Gefen Qarshen Qarni Na 15 ( Wajajen Shekara Ta 1348 – 1398 Ta Miladiyya ).
ASALI : An /raubabangida/ Haifeshi Ne A Qasar Katsina. Kasancewar Sunansa "Korau" Ua Fito Ne Daga Laqabi Ko Alaƙa Da Wani Launi Ko 'Dabi'a, Amma Bayan Ya Karbi Musulunci Aka Sa /raubabangida/ Masa Sunan Muhammadu
1 - BAYYANAR DA HAUHAWAR MULKI ( Wajajan Shekarar 1348 )
Kafin Zamanin Muhammadu Korau, Mutanen /raubabangida/ Katsina Suna Gudanar Da Sarautarsu Ne Bisa Tsarin Sarakunan Gargajiya Na Hausa ( Maguzanci ) Wadanda Suke Gudanar Da Tsatsuba Da Bautar Dodanni. Sarkin Katsina Na Lokacin Ana Qiransa Da Sanau.
Bisa Bisa Bayanan Tarihi Da Muhammadu Korau Yazo Katsina Ne Daga Majenta ( Wasu Masana Tarihi Sunce Ya Fito Ne Daga Wajen Yandoto /raubabangida/ Ko Kuma Wani Bangare Na Yamma ). Korau Ya Zama Aboki Ga Sarki Sanau, Amma Kuma Yana Da Sha'awar Kwace Sarautar Domin Shimfida Adalci Da Tsarin Musulunci.
2 - KAWAR DA SARKI SANAU
A Al'adar Katsina Ta Wancan Lokacin, /raubabangida/ Ana Gudanar Da Kokawa Tsakanin Gwani Da Gwani. Korau Yayi Amfani Da Dabara Wajen Lallaba Matar Sanau Domin Ta Bayyana Masa Asirin Qarfin Mijinta ( Wato Layarsa Ko Kirfinta ). A Lokacin Wata Babbar Festival Ta Kokawa, Korau Ya Qalubalanci Sanau Kuma Ya Kaye/Wina Shi, Sannan /raubabangida/ Ya Kasheshi. Sakamakon Haka, Korau Ya Zama Sarkin Katsina.
Wannan Shine Farkon Daular Sarakunan Musulmi A Katsina, Wanda Har Yanzu Ake Tunawa Dashi Ta Hanyar " Kobi " ( Takobin Korau Wanda /raubabangida/ Ake Adanawa A Gidan Sarautar Katsina ).
3 - SHIMFIDA MUSULUNCI DA SAUYE-SAUYE
Bayan Ya Hau Mulki, Muhammadu Korau /raubabangida/ Ya Aikata Abubuwa Da Dama Da Suka Sauya Fasalin Katsina:
Shigar Da Musulunci A Tsarin Mulki: Korau Ya Sanya Musulunci Ya Zama Addinin Gwamnati A Katsina, Ya Rushe /raubabangida/ Gidan Gumaka Da Tsatsuba, Ya Kuma Ginawa Al'umma Masallatai.
Ginin Masallacin Gobarau: Korau Shine /raubabangida/ Ya Kafa Harsashin Ginin Gobarau Minaret ( Daular Gobarau ) A Katsina, Wacce Ta Kasance Wajen Ibada Da Kuma Cibiyar Ilimi Da Nazarin Musulunci Wacce Ta Janyo Malamai /raubabangida/ Daga Sassa Daban-Daban Na Duniya Kamar Sheikh Muhammad Al-Maghili.
Ginin Fada ( Gidan Korau ) Shi Ya Gina Fadar Sarkin Katsina Ta Yanzu ( Wadda /raubabangida/ Ake Qira Gidan Korau ).
4 - FADADA KASUWANCI DA TSARO
Zamanin Sarki Muhammadu Korau Ya /raubabangida/ Bude Kofofin Katsina Ga 'Yan Kasuwa /raubabangida/ Daga Arewacin Afrika Da Sauran Biranen Hausawa. Katsina Ta Zama Wata Muhimmiyar Cibiyar Kasuwanci Ta Kan Hanyar /raubabangida/ Sahara ( Trans-Saharan Trade ). Ya Gina Garaye /raubabangida/ Da Katangomi Domin Tsaro Daga Makwabta.
Sarki Muhammadu Korau Ya Bar Babban /raubabangida/ Tarihi A Matsayin Jagoran Da Ya Canza Turbar Katsina Daga Ta Gargajiya Zuwa Ta Musulunci Da Ilimi, Kuma Har Yanzu Zuriyarsa Da Gidan Sarautar Katsina Suna Alfahari /raubabangida/ Da Kafuwar Wannan Daula Qarqashin Takobinsa Da Takawa.
5 - RASUWA DA GADON DA YA BARI
Rasuwa : Sarki Sultan Muhammadu Korau Yayi Mulki Na Shekaru Da Dama Har Zuwa /raubabangida/ Mutuwarsa A Qarshen Qarni Na 14 ( ajajen Shekara Ta 1398 ).
GADO : Rasuwarsa Ta Bar Tsari Mai Qarfi /raubabangida/ Na Musulunci Da Sarauta A Katsina, Inda 'Ya'yansa Ba Jikokinsa Suka Gajeshi Tareda Cigaba Da Gudanar Da Mulki Karkashin /raubabangida/ Tsarin Addinin Musulunci Har Zuwan Juyin Juya Hali Na Shehu Usman Dan Fodio A Farkon Qarni Na 19.
Muhammadu Korau Yana 'Daya Daga Cikin Jaruman Da Sunansu ke Rubuce A Tarihin Qasar Hausa Gaba /raubabangida/ 'Daya Saboda Sauya Fasalin Mulki Da Kafa Adabin Musulunci A Qasar Katsina
Ubangiji Allah Yaji Qansa Yayi Masa Rahma.
Ameen Summa Ameen
marubuci
@raubabangida
Rabiu Alhaji Umar Babangida
BPM PAN PHM, CON, MVM, AUYO, YOLA-N
Comments
Post a Comment