TAQAITACCEN TARIHIN SARKI SULTAN MUHAMMADU RUMFA


@@@@ @@@@ @@@@ @@@@
بسم الله الرحمن الرحيم
والصلاة والسلام على أشرف أنبياء سيدنا ومولانا محمد النبي، وعلى أزواجه أمهات المؤمنين وذريته وأهل بيته الطاهرين وصحابته الأكرمين وعلينا معهم أجمعين
@@@@ @@@@ @@@@ @@@@

Ina Qara Godewa Allah Bisa Kasantuwar Musulunci Addinina, Annabi Muhammad SAW Annabi Na, Al-qur'ani Da Hadisi Littatafaina Tsarkaka, Ka'aba Ash-sharifah Alqiblata, Malikiyyah Mazhabata, Ash'ariyyah Aqidata Ta Sunnah, Sufanci Matafiyata, Qadiriyyah Dariqata, Hausa Qabilata.

Aslm
Ya 'Yan,uwana Musulmai Maza Da Mata Manya Da Qanana Da Fatan Kowa Yana Qoshin Lafiya, Marasa Lafiyanmu Na Gida Da Na Asibiti Ubangiji Allah Ya Basu Lafiya, Masu Lafiya Kuma Allah Ya Qara Musu Lafiya, Iyayenmu Da Kakanayenmu Yayyunmu Da Qannanmu, Da Suka Rigamu Gidan Gaskiya Ubangiji Allah Yaji Qansu Yayi Musu Rahma, Muma In Tamu Tazo Allah Ya Sa Mu Cika Da Imani.
Ameen Summa Ameen
*** *** *** *** *** *** *** *** ***

SARKI SULTAN MUHAMMADU RUMFA
( Sarkin Kano Na 021 )
Yana 'Daya Daga Cikin Sarakunan Kano /raubabangida/ Mafiya Shahara, Tasiri, Da Kawo Sauye-Sauye A Tarihin Masarautar Kano Gaba Daya. Mulkinsa ( 1463–1499 ) Ana Yi Masa Kallon " Zamanin Zinare " Na Kano /raubabangida/ Saboda Manyan Cigaban Da Ya Kawo Ta Fannin Gudanar Da Mulki, Tattalin Arziki, Tsaro, Da Bunkasa /raubabangida/ Addinin Musulunci.

Haihuwa Da Farkon Rayuwa
An Haifi Muhammadu Rumfa A Tsakiyar /raubabangida/ Qarni Na 15 A Cikin Gidan Sarautar Kano. Shi 'D Ne A Gidan Sarauta Kuma Jikan Sarki Kanajeji. Ya Taso Ne A Cikin Yanayi Na Koyon Dabarun Jagoranci, Al'adun Hausawa, Da Kuma Tushen Addinin Musulunci /raubabangida/ Wanda Yake Kara Shiga Shiyyar Qasar Hausa A Wancan Lokacin.

Hawansa Mulki (1463)
Muhammadu Rumfa Ya Karbi Karagar /raubabangida/ Mulkin Kano A Shekara Ta 1463. A Lokacin Da Ya Hau Mulki, Ya Tarar Da Kano A Matsayin Gari Mai Bunqasa, Amma Yayi Amfani Da Hangen Nesansa Wajen Maida Kano Babbar Cibiyar Kasuwanci, Ilimi, Da Sarauta A Duk Fadin Yammacin /raubabangida/ Afirka.

Muhimman Ayyuka Da Gudunmawar Da Ya Bar Baya
Gina /raubabangida/ Fadar Kano ( Gidan Rumfa ): Shine Ya Gina Babbar Fadar Kano Da Ake Amfani Da Ita Har Zuwa Yau, Wadda Ake Qira Gidan Rumfa. Ya Bar Tsohuwar Fadar Dake Kusa Da Dutsen Dala Ya Koma Sabuwar Fadar /raubabangida/ Domin Fadada Cibiyar Gudanar Da Mulki.

Kafa Kasuwar Kurmi : Domin Habaka Tattalin Arziki Da Kasuwancin Saharan ( Trans-Saharan Trade ), Rumfa Ya Kafa Shahararriyar Kasuwar Kurmi A Tsakiyar /raubabangida/ Birnin Kano, Wadda Ta Zama Babbar Cibiyar Kasuwanci Ta Duniya A Lokacin.

Karfafa /raubabangida/ Addinin Musulunci : A Zamaninsa Ne Masanin ilimin Musulunci Daga Arewacin Afirka, Sheikh Muhammad Al-magili, Ya Ziyarci Kano. Al-magili Ya Rubuta Masa Littafi Mai Suna " Taj al-Din fi ma Yajib 'ala al-Muluk " ( Gidandamar Sarakuna ), Wanda Ya Zama Tsarin Mulki /raubabangida/ Da Jagoranci Mai Zaman Kansa Wajen Shimfida Adalci.

Fadada Katangar Kano Da Kofofi: Ya Fadada Katangar Birnin Kano Tare De Bude Sababbin Kofofi Domin /raubabangida/ Inganta Tsaro Da Sahalewa Baki Shigowa Gari.

Kafa Majalisar Tara ( Tara Ta Kano ) Ya Tsara Gudanar Da Mulki Ta Hanyar /raubabangida/ Kafa Majalisar Shawara Ta Sarki Mai Mutane Tara ( Council Of Nine ), Wacce Ta Qunshi Muhimman Masu Rike Da Sarautu Domin Tattauna Al'amuran Qasa.

Dabarun Yaqi Da Kayan Sarauta: Shine /raubabangida/ Ya Gabatar Da Amfani Da Dawakai Sanye Da Rigar Qarfe ( lifidi ), Da Sababbin Dabarun Tura Dakaru A Fagen Daga, Gami Da Gabatar /raubabangida/ Da Kakaki Da Sauran Kayan Kawai Na Mutuncin Sarauta.

MUTUWA / RASUWA
Bayan Ya Shafe Shekaru 36 Yana Mulki /raubabangida/ Cikin Nasara, Bunqasa Ilimi, Da Gina Qasa, Sarki Muhammadu Rumfa Ya Rasu A Shekara Ta 1499.

Rasuwar /raubabangida/ Tasa Ta Bar Gurbi Babba, Amma Gado Da Ginshikan Da Ya Kafa Daga Gidan Rumfa, Kasuwar Kurmi, Zuwa Tsarin Sarautar Kano Suna /raubabangida/ Nan Daram Har Zuwa Yau A Matsayin Shaida Ta Gudunmawar Da Ya Bayar.

    marubuci
@raubabangida
Rabiu Alhaji Umar Babangida
BPM PAN PHM, CON, MVM, AUYO, YOLA-N

Comments

Popular posts from this blog

TAQAITACCEN TARIHIN DAULAR AUYO

HAPPY BIRTHDAY TO YOU OUR DEAR FATHER, 13 APRIL

YAU SHEKARA GOMA DA RASUWA MAMANA