TAQAITACCEN TARIHIN RAYUWAR JONATHAN DA MULKINSA

DR. GOODLUCK AZIKIWE EBELE JONATHAN
@@@@ @@@@ @@@@ @@@@
بسم الله الرحمن الرحيم
والصلاة والسلام على أشرف أنبياء سيدنا ومولانا محمد النبي، وعلى أزواجه أمهات المؤمنين وذريته وأهل بيته الطاهرين وصحابته الأكرمين وعلينا معهم أجمعين
@@@@ @@@@ @@@@ @@@@

Ina Qara Godewa Allah Bisa Kasantuwar Musulunci Addinina, Annabi Muhammad SAW Annabi Na, Al-qur'ani Da Hadisi Littatafaina Tsarkaka, Ka'aba Ash-sharifah Alqiblata, Malikiyyah Mazhabata, Ash'ariyyah Aqidata Ta Sunnah, Sufanci Matafiyata, Qadiriyyah Dariqata, Hausa Qabilata.

Aslm
Ya 'Yan,uwana Musulmai Maza Da Mata Manya Da Qanana Da Fatan Kowa Yana Qoshin Lafiya, Marasa Lafiyanmu Na Gida Da Na Asibiti Ubangiji Allah Ya Basu Lafiya, Masu Lafiya Kuma Allah Ya Qara Musu Lafiya, Iyayenmu Da Kakanayenmu Yayyunmu Da Qannanmu, Da Suka Rigamu Gidan Gaskiya Ubangiji Allah Yaji Qansu Yayi Musu Rahma, Muma In Tamu Tazo Allah Ya Sa Mu Cika Da Imani.
Ameen Summa Ameen
*** *** *** *** *** *** *** *** ***

Goodluck Ebele Azikiwe Jonathan Gogaggen 'Dan Siyasar Nijeriya Ne Wanda Ya /raubabangida/ Kasance Shugaban Qasar Nijeriya Daga Shekarar 2010 zuwa 2015. Ya Kafa Tarihin Kasancewa Shugaban Qasa Na Farko A Nijeriya Da Ya Yarda Da Qaddara Sannan Ya Taya Abokin Hamayyarsa Murna A Lokacin Da Ya Faɗi Za6e, Lamarin Da Ya Kare Mutuncin /raubabangida/ Dimokuraɗiyyar Qasar.

1 - Haihuwa Da Quruciya
Rana Da Wuri : An Haifi Goodluck Jonathan /raubabangida/ A Ranar 20 Ga Nuwamba, 1957 A Qauyen Otuoke Da Ke Jihar Bayelsa A Yanzu.

Iyali : Mahaifinsa Lawrence Ebele Jonathan Ya Kasance Mai Sana'ar Qera Jiragen Ruwa Na Gargajiya, Ita Kuma /raubabangida/ Mahaifiyarsa Eunice Ayi Afeni Manoma Ce.

Suna : Mahaifinsa Ne Ya Sa Masa Suna Goodluck ( Sa'a Mai Kyau ) Saboda /raubabangida/ Jin Daɗin Samunsa, Yayin Da Kakarsa Tasa Masa Sunan Azikiwe.

2 - Karatu Da Aiki
Primary Da Secondary : Yayi Karatunsa Na Primary Da Secondary A Jihar /raubabangida/ Rivers ( Lokacin Jihar Bayelsa Tana Qarqashin Rivers ).

Jami'a : Ya Halarci Jami'ar Port Harcourt Inda Yayi Karatun Digirinsa Na Farko A Fannin Ilimin Halittar Dabbobi ( Zoology ), Sannan Ya Cigaba /raubabangida/ Da Karatun Digiri Na Biyu ( M.Sc ) Dana Uku ( Ph.D ) A Fannin Hydrobiology And Fisheries Biology.

Aiki : Kafin Shiga Siyasa, Yayi Aiki A Matsayin Malamin Makaranta, Jami’in Kiyaye Muhalli ( Environmental Protection Officer ), Kuma /raubabangida/ Ma’aikaci A Hukumar Rage Radadin Talauci Ta Yankin Manjo ( OMPADEC ).

3 - Fayil 'Din Siyasa Da Mukamai
i - Mataimakin Gwamna Da Gwamnan Jihar Bayelsa (1999 - 2007 )
A Shekarar 1999, Ya Zama Mataimakin Gwamnan Jihar Bayelsa Qarqashin Tsarin Jam’iyyar PDP Tare Da Gwamna Diepreye Alamieyeseigha.

A Watan Disamba Na Shekarar 2005, Ya Kar6i Mulkin Jihar Bayelsa A Matsayin Gwamna Biyo Bayan Tsige /raubabangida/ Alamieyeseigha Daga Mukaminsa.

ii - Mataimakin Shugaban Qasa ( 2007 – 2010 )
A Za6en /raubabangida/ Shekarar 2007, Jam'iyyar PDP Ta Zaɓeshi A Matsayin Abokin Takarar Marigayi Umar Musa Yar'Adua. Suka Sami Nasarar Lashe Za6e, Ya Kuma Rantsar /raubabangida/ Dashi A Matsayin Mataimakin Shugaban Qasa.

iii - Kar6ar Mulki ( 2010 )
Sakamakon Rashin Lafiyar Shugaba Yar'Adua, Majalisar Qasa Ya Ayyana Goodluck Jonathan A Matsayin Rukunan /raubabangida/ Shugaban Qasa ( Acting President ) A Watan Fabrairun 2010.

Bayan Rasuwar Yar'Adua A Ranar 5 Ga Mayu, 2010, An Rantsar Da Jonathan A Matsayin Shugaban Qasar /raubabangida/ Nijeriya A Ranar 6 Ga Mayu, 2010.

4 - Zamaninsa A Matsayin Shugaban Qasa ( 2010 – 2015 )
Jonathan ya Lashe Za6en Shugaban Qasa /raubabangida/ Na Shekarar 2011 Don Cigaba Da Jagorancin Qasar.

Muhimman Nasarori A Mulkinsa:
Tattalin Arziki : A Zamanin Mulkinsa (2014) An Sake Lissafa Tattalin Arzikin Nijeriya ( Rebasing Of GDP ), Wanda /raubabangida/ Yasa Nijeriya Ta Zama Qasa Ta 'Daya Mafi Qarfin Tattalin Arziki A Nahiyar Afirka.

Wutar Lantarki Da Jiragen Ƙasa : Ya Kafa Dokar Power Sector Reform Act Don Ba Bangaren Masu Zaman Kansu Damar Zuba Jari A Wutar Lantarki, /raubabangida/ Sannan Ya Farfaɗo Da Tsarin Jiragen Qasa Na Zamani ( Kamar Layin Jirgin Abuja Zuwa Kadunar ).

Zambiyantar Da Noma : Ministan Nomansa Na Waccan Lokacin ( Akinwumi Adesina ) Ya Bullo Da Tsarin Raba Takin Zamani Ta Wayar Hannu ( E-Wallet System ), Wanda Ya Rage /raubabangida/ Cin Hanci A 'Bangaren Noma.

Za6e Mai Tsabta : Ya Nada Prof. Attahiru Jega A Matsayin Shugaban INEC, Wanda Ya Gabatar Da Katin Za6e /raubabangida/ Na Zamani ( Permanent Voter Card - PVC ) Da Na'urar Card Reader.

Qalubale A Mulkinsa :
Matsalar Tsaro ( Boko Haram ): Mulkinsa Ya Fuskanci Mummunan Hare-Haren /raubabangida/ Sace 'Yan Mata A Makarantar Chibok A Shekarar 2014 Da Kuma Qwace Wasu Yankuna A Arewa Maso Gabas Da Qungiyar Boko Haram Ta Yi.

Rage Tallafin Fetur ( Subsidy Removal ) : Yunkurinsa Na Cire Tallafin /raubabangida/ Fetur A Watan Mutane Na Shekarar 2012 Ya Haifar Da Zanga-Zangar " Occupy Nigeria " A Faɗin Qasar.

Zargin Cin Hanci : Gamnatin Sa Ta Fuskanci Qalubalen Zargin 'Bataccen Kudin Mai Daga Lambobi Daban-Daban Da Kuma Qorafe-Qorafe A Kan Gudanar /raubabangida/ Da Kudaden Tsaro.

5 - Za6en 2015 Da Sadaukarwa
A Za6en Shugaban Qasa Na Shekarar 2015, Goodluck Jonathan Ya Shiga /raubabangida/ Takara Qarqashin PDP Amma Janar Muhammadu Buhari Na Jam'iyyar APC Yayi Nasara A Kansa.

Kafin /raubabangida/ Ma A Gama Qiddige Sakamakon Za6en A Hukumance, Jonathan Ya Qira Buhari Ra Wayar Hannu Ya Taya Shi Murna. Wannan Matakin Ya Ceto Nijeriya Daga Rikicin Siyasa Ya Kuma Sa Aka Yi Masa /raubabangida/ Kallo A Matsayin Jarumin Dimokuraɗiyya A Afirka. Shahararriyar Maganarsa Itace:

" Cimma Nasarar Sanya Burina Bai Kai Darajar Zubar Da Jinin Kowani 'Dan Nijeriya Ba "

6 - Rayuwarsa Daga 2015 Zuwa Yanzu
Bayan /raubabangida/ Barinsa Mulki A Shekarar 2015, Jonathan Ya Maida Hankali Kan Aikace-Aikacen Qasa Da Qasa:

Jakadan Zaman Lafiya : Ya Kasance Babban Mai Sa Ido A Zaɓukan Qasashe Daban-Daban A Nahiyar Afirka Qarqashin Qungiyoyin ECOWAS, AU, Da Commonwealth.

Gidauniyar Goodluck Jonathan Foundation : Ya Kafa Gidauniya Don Ha6aka /raubabangida/ Kyakkyawan Shugabanci, Peace-Building, Da Dimokuraɗiyya A Afirka.

Ya Jagoranci Tattaunawar Zaman Lafiya A Tsakanin 'Bangarorin Da Ke /raubabangida/ Rikici A Qasar Mali A Matsayin Jakaden ECOWAS.

@raubabangida
Rabiu Alhaji Umar Babangida
BPM PAN PHM, CON, MVM, AUYO, YOLA-NORTH



Comments

Popular posts from this blog

TAQAITACCEN TARIHIN DAULAR AUYO

HAPPY BIRTHDAY TO YOU OUR DEAR FATHER, 13 APRIL

YAU SHEKARA GOMA DA RASUWA MAMANA