ALHAJI IBRAHIM BADAMASI BABANGIDA GCFR
@@@@ @@@@ @@@@ @@@@
بسم الله الرحمن الرحيم
والصلاة والسلام على أشرف أنبياء سيدنا ومولانا محمد النبي، وعلى أزواجه أمهات المؤمنين وذريته وأهل بيته الطاهرين وصحابته الأكرمين وعلينا معهم أجمعين
@@@@ @@@@ @@@@ @@@@
Ina Qara Godewa Allah Bisa Kasantuwar Musulunci Addinina, Annabi Muhammad SAW Annabi Na, Al-qur'ani Da Hadisi Littatafaina Tsarkaka, Ka'aba Ash-sharifah Alqiblata, Malikiyyah Mazhabata, Ash'ariyyah Aqidata Ta Sunnah, Sufanci Matafiyata, Qadiriyyah Dariqata, Hausa Qabilata.
Aslm
Ya 'Yan,uwana Musulmai Maza Da Mata Manya Da Qanana Da Fatan Kowa Yana Qoshin Lafiya, Marasa Lafiyanmu Na Gida Da Na Asibiti Ubangiji Allah Ya Basu Lafiya, Masu Lafiya Kuma Allah Ya Qara Musu Lafiya, Iyayenmu Da Kakanayenmu Yayyunmu Da Qannanmu, Da Suka Rigamu Gidan Gaskiya Ubangiji Allah Yaji Qansu Yayi Musu Rahma, Muma In Tamu Tazo Allah Ya Sa Mu Cika Da Imani.
Ameen Summa Ameen
*** *** *** *** *** *** *** *** ***
Wannan Rubutu Zanyishi Ne Saboda Banajin Dadin Yadda Mutane Suke /raubabangida/ Hira Ko Zantuka Ko Ganin Gwamnatin IBB Na Soja, Ba Abunda Ta Tsinanawa Najeriya. Kuma Shi Mai Wannan Sunanmu Yazo 'Daya, Inkiyana Babangida, Kuma 'Dan,uwanane A Musulunce, Kuma 'Dan,uwanane /raubabangida/ A Qabila ( Hausa )
Shine Na Zauna Nace Barin In Zanyano Muku Wanene IBB Kuma Menene /raubabangida/ Gwamnatinsa Na Soja Ta Qirqira, Ta Kawo Domin Cigaban Qasa, Wadanda Wasunsu Har Yau Suna Nan Suna Aiki Kuma Ana Di6an Ma'aikata A Wannan Ma'aikatun.
Domin Sanin Taqaitaccen Wanene IBB Kuma /raubabangida/ Menene Yayi A Lokacin Gwamnatinsa, Saika Dan Ware Wasu 'Yan Mintuna Ka Karanta.
Abun Yana Fata Mini Rai, In Ana Maganar Tsofin Shuwagabannin Qasar /raubabangida/ Wadanda Suka Kawo Cigaban Qasa A Najeriya Ba'a Sanya Sunansa,
A Fahimtata Saboda Abubuwa Guda Biyu Ne ( Bazan Ambata Ba ) Yasa Ake Masa Haka
GABATARWA
Shugaba Ibrahim Badamasi Babangida, Shine Tsohon Shugaban Tarayyar Najeriya Na 8, Kuma Tsohon /raubabangida/ Sojan Najeriya Mai Ritaya Wanda Yayi Aikin Soja Tun Daga Matakin Sakan Laftanar /raubabangida/ Har Zuwa Janar.
Shugaba Ibrahim Badamasi Babangida Mutum Ne 'Dan Kishin Qasa, Jarumi, Mai Basira, Hangen Nesa, /raubabangida/ Sannan Kuma Mai Fasaha Da Kuma Qwazo Wajen Aiki, Ya Bada Gudunmawa Mai Gwa6i A Fannin Aikin Soja Tun Daga Kwamanda /raubabangida/ Har Ya Zama Shugaban Qasa.
Ya Bada Gagarumar Gudunmawa Wajen /raubabangida/ Kasantuwar Najeriya A Matsayin Qasa 'Daya, Ta Hanyar Daqile Yunqure-Yunquren Juyin Mulki Da Dama Tun Kafin Zamowarsa Shugaban Qasa. Shine Sojan /raubabangida/ Da Ya Hau Kujerar Shugabancin Najeriya Ta Hanyar Juyin Mulkin Da Ba A Zubar Da Jini Ba; Mutum Ne Da Ya Baiwa Najeriya Da ‘Yan Najeriya Gudunmawa Tun Daga Shekarar 1964 Har Zuwa 1993 A Matsayin Soja, Sannan Kuma Ya Ke Cigaba Da Bada /raubabangida/ Gudunmawa Ta Fannoni Da Dama Na Rayuwa.
Ya Kafa Hukumomin Da Har Gobe Suke Bada Guraben Ayyukan Yi A Najeriya /raubabangida/ Kamar Irinsu Hukumar Kiyaye Hadduran Kan Titi ( Federal Road Safety Corps ), Hukumar Samar Da Ayyukan Yi ( National Directorate of Employment ) Da Sauransu.
Shugaba Ibrahim Badamasi Babangida, Bayan Kasancewarsa Soja, /raubabangida/ Kuma 'Dan Siyasa Daga Baya, Malamin Addinin Musulunci Ne Wanda Yake Gudanar Da Fassarar Al-qur'ani Mai Girma Daga Gidansa A Cikin Watan Azumi Mai Albarka.
HAIHUWARSA
An Haifi Shugaba Ibrahim Badamasi Babangida A Ranar 17 Ga Watan Agusta Na Shekarar 1941, A Garin Minna /raubabangida/ Ta Jahar Neja/Niger
KARATUNSA
Shugaba Ibrahim badamasi Babangida Yayi Karatun Firamare Daga /raubabangida/ Shekarar 1950 Zuwa 1956. Sai Kwalejin Gwamnati ( Government College ) Ta Garin Bidda Daga Shekarar 1957 Zuwa 1962.
Bayan Kammala Kwaleji Sai Ya Tafi Makarantar Horas Da Sojoji Ta Najeriya ( Nigerian Military Training College ) A Ranar 10 Ga Watan Disamba /raubabangida/ Na Shekarar 1962 Zuwa Ranar 20 Ga Watan Afirilu Na Shekarar 1963.
A Shekarar 1964 Ya Samu Horo A Makarantar Horas Da Sojoji Ta Indiya ( Indian Military Academy ). Sai Kuma Makarantar Qasar Ingila Inda Ya Halarci Kwas/Course 'Din ‘Young Officer’s Course’ A ‘Royal Armoured Centre’ Wanda /raubabangida/ Ya Kammala A Watan Afirilu Na Shekarar 1966. Sai Kuma Kwas/Course 'Din ‘Armoured Driving Maintenance’ A Shekarar 1967 Duk /raubabangida/ A Royal Armoured Centre Ta Qasar Ingila.
1970 Ya /raubabangida/ Samu Halartar Kwas/Course Din ‘Company Commander’s Course’ A Warminster, Ingila Daga Watan Oktoba Zuwa Nuwamba. 1972 Yaje Armoured School Ta Amurka Inda Ya Samu Horon " Adɓanced Armoured Officer’s Course " Kwas/Course 'Din Da /raubabangida/ Ya Gama A Ranar 8 Ga Watan Yuni Na Shekarar 1973. Sai Kuma Makarantar Sojoji Ta Jaji, Ta Jahar Kaduna, Inda Ya Samu /raubabangida/ Horo Na " Senior Officer’s Course " A Shekarar 1977. Sai Shekarar 1979 Inda Ya Halarci Kwas/Course Din ‘Policy And Strategic Course’ A ‘Nigerian Institute Of Planning And Strategic Studies’ Dake Kurun Jahar Filato A Najeriya. A Shekarar 1980 Inda Ya Samu /raubabangida/ Horon ‘Senior International Defence Management’ A Qasar Amurka.
MUQAMAI
Shugaba Ibrahim Badamasi Babangida Soja Ne Da Ya Fara Daga Muƙamin Sakan Lutenant Har Ya Kai Muqamin Janar. /raubabangida/
- Sakan lutenant ( Second Lieutenant ) 20 Ga Afirilu, 1963.
- Lutenant ( Lieutenant ) 1966.
- Kyaftin ( Captain ) Watan Agusta, 1968.
- Manjo ( Major ) Afirilu, 1970.
- Laftanar Kanal ( Lieutenant Colonel ) 1974.
- Birgediya ( Brigadier ) 1979.
- Manjo Janar ( Major General ) 1 Ga Mayu, 1983.
- Janar ( General ) 1 Ga Oktoba, 1987.
GOGAYYAR AIKI
Kwamanda ( Commanding Officer ) Na ‘1st Reconnaissance Squadron’ 1964 Zuwa 1966.
Kwamandan /raubabangida/ Rundunar Soja Ta 44 ( Commander 44 Infatry ) Yuni, 1968.
Kwamandan Rundunar Soja Ta 44 ( Commander 44 Infatry ) Yuni, 1970.
Malami /raubabangida/ Kuma Kwamanda Na Makarantar Tsaro Ta Najeriya ( Instructor And Company Commander , Nigerian Defence Academy ) 1970 Zuwa 1972.
Insifecta Kuma Kwamandan Rundunar /raubabangida/ Mayaqan Tanka ( Inspector And Commander Nigerian Armoured Corps ) 1975 Da Kuma 1977 Zuwa 1979.
Mamba /raubabangida/ Na Majalisar Ƙoli Ta Soja ( Member Supreme Military Council ) 1 Ga Agusta 1975 Zuwa Oktoba 1979.
Daraktan Jami’an Sojoji ( Director Army Staff Duties And Plans ) 5 Ga Janairu, 1981.
Shugaban Rundunar Sojojin Qasan Najeriya ( Chief Of Army Staff ) 31 Ga Disamba 1983.
Ciyaman /raubabangida/ Na Majalisar Shugabanci Ta Soji ( Chairman Armed Forces Ruling Council AFRC )
Shugaban /raubabangida/ Qasar Najeriya 27 Ga Agusta Na Shekarar 1985 Zuwa 27 Ga Agusta Na Shekarar 1993.
Zamowarsa Shugaban Ƙasa
Janar Ibrahim Badamasi Babangida
Shugaba Ibrahim Babadamasi Babangida Ya Zama Shugaban Najeriya Ne /raubabangida/ A Shekarar 1985 Bayan Da Ya Qwaci Mulki Daga Hannun Shugaba Muhammadu Buhari. Yayi Wannan Juyin /raubabangida/ Mulki Ne Da Nufin Farfaɗo Da ‘Yancin 'Dan’Adam Da Ake Takewa Da Kuma Sake Farfaɗo Da Tattalin Arziqin Qasa Wanda Ya Shiga Mayuwacin Hali, Kamar /raubabangida/ Yadda Yazo A ( Ajaegbu, Matthew-Daniel, Da Uya, 2000; Olawale, 2014 ).
Gudunmawar Gwamnatinsa
Marubuta Da Dama, (CNwabugo, 2011; Abdullahi, Hussain Da Abdullahi, 2012; Alison, 1993 ; 2016 ; Pate, 2013 ), Sunyi Rubuce-Rubuce Masu Tarin Yawa /raubabangida/ Dangane Da Nagarta Da Kyawawan Manufofi Da Kuma Gudunmawa Mai Gwaɓi Da Wannan Gwamnati Ta Shugaba Ibrahim Badamasi Babangida Ta Bayar A Zamanin Mulkinta Duk Da Irin Matsaloli Taci Karo Dasu Musamman A Qarshen Mulkinta. Alison ( 1993 ), Ta Bayyana Cewa Shirin Gwamnatin Shugaba Ibrahim Badamasi Babangida Ya Nuna Cewa Gwamnatin /raubabangida/ Tayi Qoqarin Da Dukkan Gwamnatocin Da Suka Gabace Ta Basu Yi Ba Dangane Da Ha66aka Tattalin Arziqin Najeriya, Inda Ta Bayyana Cewa Tabbas Daidaikun Mutane Sun Fuskanci Rashin /raubabangida/ Kudi Amma Tattalin Arziƙin Qasar Ya Cigaba. Kadan Daga Cikin Irin Wadannan Gudunmawowi Akwai:
01 - Shigo Da Jama’a Harkokin Mulki : Duk /raubabangida/ Da Kasancewar Gwamnatin Shugaba Ibrahim Badamasi Babangida Ta Soja; Wacce Ake Yiwa Kallon Kama-Karya, Ta Tuntu6i Jama’ar Najeriya Dangane Da Ra’ayinsu Kan Kar6ar Lamani Daga Asusun Bada Lamani Na Duniya IMF) Wanda Aka Fara Tattaunawa Tun Gwamnatin Farar Hula Ta Shugaba Shehu Shagari, Sannan /raubabangida/ Kuma Gwamnatin Soja Ta Shugaba Muhammadu Buhari Ta 'Dora.
A Nan, Wadanda Basu Yarda Da Kar6o Bashin Ba, Su Suka Fi Rinjaye, Saboda /raubabangida/ Haka Sai Shugaba Ibrahim Badamasi Babangida Ya Janye Maganar.
02 - Fito Da Tsarin ‘Structural Adjustment Programme’, Wato SAP A Taqaice. Nuna Rashin Amincewar ‘Yan Najeriya Kan Kar6o Waccan Bashi, /raubabangida/ Sai Shugaba Ibrahim Badamasi Babangida Ya Fito Da Wannan Shiri, Dan Ingantawa Tare Kuma Da Ha66aka Tattalin Arziƙin Najeriya. Wannan Tsari Na SAP, Yana /raubabangida/ Da Manufofin Da Suka Hada Da :
Rage Yawan Kudaden Da Gwamnati Ke Kashewa Wajen Bayar Da Tallafi Kan Albarkatun Mai.
Samar /raubabangida/ Da Hanyoyin Dogaro Da Kai; Wato Ya Zama Ita Qasar Ta Dogara Da Kanta Ta Fuskanci Samar Da Wasu Abubuwa Na More /raubabangida/ Rayuwa Sa6anin Dogaro Da Wasu Qasashen Qetare.
Toshe Gi6in Da Ake Samu A Qasafin Kudin Najeriya.
Rage Dogaro Da Shigo Da Kayayyaki Da Kuma /raubabangida/ Albarkatun Mai A Matsayin Babbar Hanyar Samun Kudaden Shiga.
Ha66aka Nagartar Masana’antu Masu Zaman Kansu Dan Su Zama Masu Samar Da Cigaba.
Inganta /raubabangida/ Harkokin Masana’antun Gwamnati Ta Hanyar Sayar Da Qadarorin Gwamnati Dan Su Koma Masu Zaman Kansu, Wanda Wannan Shine Ya Kafa Tubalin Sayar Da Kamfanin Sadarwa Na Najeriya ( NITEL ) Wanda Yanzu Ya Zama /raubabangida/ Kafa Ta Samun Kudaden Shiga Da Kuma Samun Kafofin Sadarwa Da Dama Ta Hanyar Baiwa Kamfanonin Sadarwa Irinsu MTN, GLO, Da Sauransu Damar Zuba Jarinsu Kamar Yadda Ake Iya Gani.
03 - Qiroqiro Sababbin Jahohi Guda Goma-Sha-Daya Babbar Manufar
( Kamar Su Katsina Da Akwa Ibom A 1987, Sai Su Jigawa, /raubabangida/ Kano, Kebbi, Taraba, Da Sauransu A 1991) Don Rarraba Iko, Wannan Shiri Itace Kusanta Gwamnati Da Jama’a Da Kuma Kusantar /raubabangida/ Da Jama’a Ga Gwamnati Da Kuma Uwa-Uba Samar Da Guraben Ayyukan Yi.
04 - Kafa Hukumar Ha66aka Aikin Gona Da Albarkatun Qasa ( Nigerian Agricultural And Land Development Authority NALDA ) Qarqashin Wannan Hukuma Aka Qirqiri Hukumomi /raubabangida/ Masu Yawa A Fadin Tarayyar Najeriya Wadanda Suke Kula Da Inganta Harkokin Noman Rani Ta Hanyar Samarwa Tare Kuma Da Kula Da Fadamu.
05 - Kafa Hukumar Inganta Rayuwar Matan Karkara ( Better Life For Rural Women )
06 - Hukumar Wayar Da Kan Jama’a Game Da Farfaɗo Da Tattalin Arziƙi, Dogaro Da Kai, Da Kuma Adalci ( Mass Mobilisation For Economic Recoɓery, Self-Reliance And Social Justice MAMSER ) A Watan Agusta Na /raubabangida/ Shekarar 1987.
07 - Kafa Kwamitin Sabunta Tsarin Mulki ( Constitution Review Committee ) Satumba 1987.
08 - Kafa Hukumar Za6e ( National Electoral Commission NEC ) Disamba 1987.
09 - Dawo Da Babban Birnin Tarayya Zuwa Abuja A Shekarar 1991.
10 - Kafa Hukumar DEFFRI, Hukumar Da Ke Kula Da Harkar Abinci, Gina Hanyoyi Da Kuma Sauran Kayan More Rayuwa A Yankunan Karkara.
11 - Hukumar Samar Da Ayyukan Yi ( National Directorate For Employment NDE ) Hukuma Ce Da Ta Riqa Koyar Da Sana’o’i Ga ‘Yan Najeriya Dan A Samu Ayyukan Yi. Wannan /raubabangida/ Hukuma Tana Da Cibiyoyi Da Makarantu Da Har Ta Kai Ga Akwai Motoci Masu Tsarin Makaranta Da Suke Shiga Qauyuka Dan Koyar Da Sana’o’i.
12 - Hukumar Kiyaye Haɗɗuran Kan Titi ( Federal Road Safety Commission ( FRSC ) Tabbas Wannan Hukuma Tana Bayar Da Gudunmawa Ta Fuskokin Da Suka Hada Da Samar Da Ayyukan Yi, Tara Kudaden /raubabangida/ Shiga Ga Gwamnati, Rage Afkuwar Haɗɗura Ta Hanyar Tuqin Ganganci, 'Daukar Majinyatan Hadari Zuwa Asibitoci, Da Sauransu.
13 - Bankin Al’umma ( Peoples Bank ) Banki Ne Da Aka Kafa Shi Da Nufin /raubabangida/ Taimakawa Qananan ‘Yan Kasuwa Su Samu Rance Ba Tare Da Sun Bayar Da Fansa Ga Wannan Banki Yanzu Babu Shi.
14 - Bankin Kwamuniti ( Community Bank ).
15 - Inganta Albashin Ma’aikata.
16 - 'Daukaka Darajar Najeriya Daga Matsayin Mai Saka Ido Ya Zuwa Cikakkiyar Mamba A Zauren Haɗin Kan /raubabangida/ Qasashen Musulmi ( Member Organization Of Islamic Conference ( OIC ), A Watan Janairu Ba Shekarar 1986.
17 - Kafa Kwamatin Kula Da Miƙa Mulki Ga Hannun Farar Hula.
18 - Ya Qirqiri Jam’iyyun Siyasa Guda Biyu Waɗanda Aka Yiwa Sakatariyoyi A Dukkan Jahohi Da Qanan Hukumomin Najeriya Na Lokacin; Gine-Ginen Da Aka Riqa Maida /raubabangida/ Wasunsu Makarantu, Asibitoci, Da Sauran Ma’aikatun Gwamnati A Halin Yanzu.
19 - Kyautata Dangantakar Najeriya Da Ƙasashen Waje: Gwamnatin Shugaba Ibrahim Badamasi Babangida Ta Inganta Dangantakar Najeriya /raubabangida/ Da Qasashen Waje Kamar Haka:
Farfaɗo Da Dangantaka Tsakanin Najeriya Da Ingila : A Watan Janairun 1986, Shugaba Ibrahim Badamasi Babangida Ya Gyara Dangantakar Najeriya Da Qasar Birtaniya Bayan Da Ta /raubabangida/ Taɓarɓare A Lokacin Gwamnatin Da Ta GabaceTa.
Gwamnatin Shugaba Ibrahim Badamasi Babangida Ta Bayar Da Gagarumar Gudunmawa Wajen Wanzar Da Zaman Lafiya A Wasu Daga /raubabangida/ Cikin Qasashen Afirka Ta Yamma, Ta Hanyar Amfani Da Rundunar Sojin Hadin-Guiwa ( ECOMOG ), Musamman A Qasashe Irinsu Laberiya ( Liberia ).
BUDE BODA / BORDER
A Ranar 28 Ga Watan Fabarairu Na Shekarar 1986, An Bude /raubabangida/ Bodidin Najeriya Da Gwamnatin Da Ta Gabace Ta, Ta Rufe.
Shirin Bayar Da Tallafin Fasaha ( Technical Aid Corp Scheme ) Shiri Ne Da Ake Tura Matasan Najeriya Dan Bada Gudunmawa A Wata Qasa Mabuqaciya A Cikin Nahiyar Afirka Da Yankin Karebiya. Tabbas Wannan Shiri Ya /raubabangida/ Samar Da Guraben Ayyukan Yi Ga Dimbin ‘Yan Najeriya A Qasashen Waje. Qarqashin Wannan Shirin Matasan Da Suka Samu Horo A Fannonin Kimiyya, /raubabangida/ Fasaha, Lafiya, Shari’a ( Science, Technology, Engineering, Law, ETC ) Da Sauranu, Su Ake Turawa Wadannan Qasashe Mabuqata Dan Bayar Da Gudunmawa Ta Tsawon Shekaru Biyu.
Barinsa Kujerar Shugabancin Najeriya
Bayan Soke Za6en Ranar 12 Ga Watan /raubabangida/ Yuni Na Shekarar 1993 Da Gwamnatin Shugaba Ibrahim Badamasi Babangida Tayi, Abubuwa Sun Cukurkude Ta Yadda Har Sai Da Ta Kai Shi /raubabangida/ Barin Wannan Kujera Ta Shugabancin Najeriya A Ranar 27 Ga Watan Agusta Na Shekarar 1993, Inda Ya Miqa /raubabangida/ Mulki A Hannun Gwamnatin Riqon Qwarya Shugaba Ibrahim Badamasi Babangida Ya Jagoranci Najeriya Tsawon /raubabangida/ Shekaru 8 Cif-Cif, Inda Ya Hau A Ranar 27 Ga Watan Agusta Na 1985, Ya Kuma Sauka A Ranar 27 Ga Watan Agusta Na Shekarar 1993, Shekaru 8 Kenan Cif-Cif, Da Dadi Ba Ragi.
SIYASAR SA
Shugaba Ibrahim Badamasi Babangida 'Dan Siyasa Ne Wanda Yake Mamba A Jama’iyyar PDP. Yayi Yunqurin /raubabangida/ Tsayawa Takarar Kujerar Shugabancin Najeriya A Wannan Jama’iyya Inda Ya Yanki Fom 'Din Tsayawa Takara A Ranar 8 Ga Watan Nuwamba Na Shekarar 2006 Dan Tsayawa Takarar 2007, Amma Daga Baya Ya Janye Saboda Fitowar Marigari Umaru Musa ‘Yar’aduwa Da /raubabangida/ Kuma Janar Aliyu Gusau
Sannan Kuma Ya Sake Yunqurin Tsayawa Takarar A Shekarar 2011, Inda Ya Fara Da Qaddamar Da Shafin Intanet /raubabangida/ Domin Kamfen 'Dinsa. Shima Daga Baya Ya Janye Saboda Qoqarin Ra6a Aukuwar Fashewar Bom A Abuja Da Akeyi Da Shi
IYALI
Shugaba Ibrahim Badamasi Babangida Ya Auri Marigayiya Maryam /raubabangida/ A Ranar 6 ga Watan Satumba Na Shekarar 1969, Sun Haifi ‘Ya’ya Hudu Biyu Maza ( Muhammad Da Aminu ), Biyu Kuma Mata ( Aisha Da Halima ).
KYAUTUTTUKAN YABO DA GIRMAMAWA
Shugaba Ibrahim Badamasi Babangida Ya Kar6i Kyaututtukan Yabo /raubabangida/ Da Girmamawa A Ciki Da Wajen Najeriya Masu Tarin Yawa. Daga Ciki Akwai:
- Lambar yabo ta CFR
Commander Of Federa Reupblic Of Nger.
- Lambar Yabo Ta DSM
Defence Service Medal.
- Lambar Yabo Ta NSM
National Service Medal.
-:Lambar Yabo Ta RSM
Royal Service Medal.
- Lambar Yabo Ta GSM
General Service Medal.
- Lambar Yabo Ta GCFR
Grand Commander Of The Federal Republic.
@raubabangida
Rabiu Alhaji Umar Babangida
BPM PAN PHM, CON, MVM, AUYO, YOLA-NORTH
Comments
Post a Comment