005 TAQAITACCEN BAYANI AKAN SALLAN JUMA'AH

kashi na 5
@@@@ @@@@ @@@@ @@@@
بسم الله الرحمن الرحيم
والصلاة والسلام على أشراف أنبياء سيدنا ومولانا محمد النبي وعلى أزواجه أمهات المؤمنين وذريته وأهل بيته الطاهرين وصحابته الأكرمين وعلينا معهم أجمعين
@@@@ @@@@ @@@@ @@@@

Ina Qara Godewa Allah Bisa Kasantuwar Musulunci Addinina, Annabi Muhammad SAW Annabi Na, Al-qur'ani Da Hadisi Littatafaina Tsarkaka, Ka'aba Ash-sharifah Alqiblata, Malikiyyah Mazhabata, Ash'ariyyah Aqidata Ta Sunnah, Sufanci Matafiyata, Qadiriyyah Dariqata, Hausa Qabilata.

Aslm
Ya 'Yan,uwana Musulmai Maza Da Mata Manya Da Qanana Da Fatan Kowa Yana Qoshin Lafiya, Marasa Lafiyanmu Na Gida Da Na Asibiti Ubangiji Allah Ya Basu Lafiya, Masu Lafiya Kuma Allah Ya Qara Musu Lafiya, Iyayenmu Da Kakanayenmu Yayyunmu Da Qannanmu, Da Suka Rigamu Gidan Gaskiya Ubangiji Allah Yaji Qansu Yayi Musu Rahma, Muma In Tamu Tazo Allah Ya Sa Mu Cika Da Imani.
Ameen Summa Ameen

*** *** *** *** *** *** *** *** ***

Insha Allahu Cikin Wannan Rubutun Zamu 'Dan 'Dauko Taqaitaccen Bayani /raujimetawiy/ Dangane Da Sallan Juma'ah Daga Littafin Fiqhun Mazhabar Malikiyyah, Sanannen Littafin Da Kowa Yasanshi, Wato ISHMAWIY Wanda AL-SHEIKH AL-IMAM AL-ALIMU AL-ALAMATU ABDUL-BARIYI AL-ASHMAWIY RUFA'IYUN Allah Yaji Qansa Da Rahma Wallafa.

A Gurguje
In Bamu Manta /raubabangida/ Ba Munce Insha Allahu Zamu Tashi A Inda Malam Mai Littafi Yake Cewa :
*

وَيَحْرُمُ:
السَّفَرُ عِنْدَ الزَّوَالِ مِن يَومِ الجُمُعَةِ عَلَى مَن تَجِبُ عَلَيْهِ الجُمُعَةُ.
Yana Haramta
Yin Tafiya /raubabangida/ Lokacin Da Rana Yayi Zawali ( Abun Nufi : Lokacin Da Rana A Matsa A Tsakiyan Sama ) A Ranar Juma'ah Ga Wanda /raubabangida/ Sallan Juma'ah Ya Wajaba Akansa

وَكَذَلِكَ يَحْرُمُ عَلَيْهِ الكَلاَمُ وَالنَّافِلَةُ وَالإِمَامُ يَخْطُبُ، سَوَاءٌ كَانَ في الخُطْبَةِ الأُوْلَى أَو الثَّانِيَةِ، 
Hakanan Yana Haramta A Gareshi Yin /raubabangida/ Magana Ko Yin Sallar Nafila A Lokacin Da Liman Yake Huduba, Sawa'un, A Hudubar Ta Farko /raubabangida/ Ko A Huduba Ta Biyu.

( Dangane Da Hani Da Yin Surutu, A Lokacin/raubabangida/ Da Liman Yake Huduba )
A Gurguje, In Muka Je 
MUWADDA MALEEK
KITABUT JUMA'ATI
BABI NA
باب مَا جَاءَ فِي الإِنْصَاتِ يَوْمَ الْجُمُعَةِ وَالإِمَامُ يَخْطُبُ: 
Hadisi Na 231 
حَدَّثَنِي يَحْيَى عَنْ مَالِكٍ عَنْ أَبِي الزِّنَادِ عَنِ الأَعْرَجِ عَنْ أَبِي هُرَيْرَةَ أَنَّ رَسُولَ اللَّهِ صَلَّى اللَّهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ قَالَ: إِذَا قُلْتَ لِصَاحِبِكَ أَنْصِتْ وَالإِمَامُ يَخْطُبُ يَوْمَ الْجُمُعَةِ فَقَدْ لَغَوْتَ.
MANZON ALLAH S.A.W YACE
Idan Kace Da Abokinka ( Na Gefenka Da Yake Surutu, A Sa'ilin Da Liman Yake Huduba ) Yi Shiru, A Lokacin Da Liman Huduba, A Ranar Juma'ah, Toh Haqiqa Yayi Lagawu.
Bayani /raubabangida/ Akan Wannan Yana Da Yawa, Sai Kuma Tuntu6i Malamai Makusanta Daku, Domin /raubabangida/ Su Qara Muku Bayani.

Dangane Da Hani Akan Yin Sallan Nafila A Yayin Da Liman Yake Huduba, /raubabangida/ A Mazhabar Malikiyyah, Ma’aunin Da Suka Dogara A Kansa Wajen Hana Yin Sallan Nafila ( Kamar Sallan Gaisuwa Ga Masallaci / Tahiyyatul Masjid ) Lokacin Da Liman Yake Hudubar Juma'a Ya Kasu Kashi Biyu: Hadisan Annabi (S.A.W) Da Kuma Aikin Sahabbai Da Malaman Madina.

1 - Hadisan Annabi (S.A.W)
Hadisin Abu Hurairah (R.A):
Annabi (S.A.W) ya ce:

"Idan ka ce wa dan uwanka 'Yi shiru' a ranar Juma'a alhalin liman yana huduba, to lallai ka yi maganar banza (kuma lada ya ragu)."
(Bukhari da Muslim)

Hujjar Malikiyyah: Domin Sauke Nauyin " Yin Shiru " Da Annabi S.A.W Yayi Umarni, Dole Mutum Ya Nutsu /raubabangida/ Da Jikinsa Da Harshensa. Tunda Ko Kalmar Gargadi Irin " Yi Shiru " An Hane Ta Domin Kar Ta Shagaltar Da Mutum Daga Sauraronsa, To Yin Salla Wanda Ya Hada Da Karatu Da Motsin /raubabangida/ Jiki Yafi Tsanani Wajen Shagaltarwa.

Hadisin Abdullahi Bin Umar (R.A):
Annabi S.A.W Ya ce:

" Idan Dayan Cikinku Ya Shiga Masallaci Ranar Juma'a, Alhalin Liman Yana Kan Mimbari, To Kada Ya Yi Salla Har Sai Liman Ya Kammala Huduba "
( Daraqudani Da Ibn Abi Shaibah )

2 - Aikin Sahabbai Da Mutanen Madina ( Amalu Ahli Madina )
Mazhabar Malikiyyah Tana Ba Aikin Malaman /raubabangida/ Madina Da Sahabbai Babbar Hujja. A Aikace, Sun Tsinci Manyan Sahabbai Irinsu Umar Bin Al-Khattab, Uthman Bin Affan, Da Ibn Umar RTA Suna Hana Mutane Yin /raubabangida/ Salla Da Zarar Liman Ya Fito Ko Ya Hau Kan Mimbari

A Wajen Malikiyyah, Fitowar Liman Zuwa Mimbari Tana Yanke Kowace Irin /raubabangida/ Salla Da Magana Har Dai An Gama Sallar Juma'a.

Su Kuma Wanda Suke Ganin Babu Damuwa /raubabangida/ Ya Halatta Ayi Sallan Nafila A Sa'ilin Da Liman Yake Huduba.

Sahihul Bukhari
17 - Kitabu Juma'ati
31 - Babu Man Ja'ah Wal Imamu Yakdubu, Sallah Rak'ataini Kafifataini
Hadisi Na 889 

حدثنا علي بن عبد الله قال: حدثنا سفيان، عن عمرو:
سمع جابرا قال: دخل رجل يوم الجمعة، والنبي صلى الله عليه وسلم يخطب، فقال: أصليت قال: لا، قال: قم فصل ركعتين
Wani Mutum Ya Shigo ( Masallaci ) Ranar Juma'ah ( A Sa'ilin / A Lokacin ) Annabi S.A.W Yana Huduba, Sai ( Annabi Ya Tambayeshi ) Shin Kayi Sallah ( Sallan Nafila ) Sai Mutumin Yace A'a ( Baiyi Ba ) Sai Annabi ( Yace Masa ) Tashi Kayi Sallah Raka'ah Biyu.

A Gurguje, /raubabangida/ Wannan Matsalace Da Take Da Fadi, Sai Aje Ga Malamai Makusanta Domin Warware Wannan Matsalar
*

وَيَجْلِسُ الرَّجُلُ وَلاَ يُصَلِّيْ، إِلاَّ أَنْ يَكُونَ تَلَبَّسَ بِنَفْلٍ قَبْلَ دُخُوْلِ الإِمَامِ، فَيُتِمُّ ذَلِكَ.
Mutum /raubabangida/ Zai Zauna ( Idan Ya Shiga Masallaci Ya Tarar Da Liman Yana Huduba ) Hakanan Bazai Yi Sallahr ( Nafila ) Ba, Sai Dai Idan /raubabangida/ Ya Fara Yin Sallahr Nafilar Ne, Liman Ya Shigo, Nan Kam Saiya Qarasar Da Sallahr Nafilarsa.
*

وَيَحْرُمُ البَيْعُ وَالشِّرَاءُ عِنْدَ الأَذَانِ الثَّانِي، وَيُفْسَخُ إِنْ وَقَعَ.
Hakanan /raubabangida/ Yana Haramta Saye Da Sayarwa A Lokacin Da Akayi Qiran Sallah Na Biyu, Kuma Za'a Warware Cinikin Koda Cinikin Ya Fada.

وَيُكْرَهُ:
تَرْكُ العَمَلِ يَوْمَ الجُمُعَةِ،
An Karhanta
Barin ( Yin Ko Qin Zuwa ) Aiki Ranar Juma'ah ( Don Ko A Yanzu Munada Mutanen Da Su Kwata-Kwata Basa Fita Aiki /raubabangida/ Ranar Juma'ah, Babu Lokacin Warware Wannan Matsalar, Amma Ko Dan Gudun Yin Kamanceceniyya Da Yahudu Da /raubabangida/ Nasara Bai Kamata Mutum Yana Qin Fita Aiki Ranar Juma'ah, Yahudawa Suna Qin Fita Aiki ( Wato Yin Hutu ) Ranar Asabar, Nasara/Kiristoci Kuma Ranar /raubabangida/ Lahadi Kai Kuma Musulmi Kace Bazaka Fita Aiki Ba Ranar Juma'ah, Kaga Ai An Samu Kamanceceniyya )

وَتَنَفُّلُ الإِمَامِ قَبْلَ الخُطْبَةِ،
Hakan ( An Karhanta ) Yin Sallahn Nafila /raubabangida/ Kafin Huduba, ( Anyi Hani Ga Liman Idan Yazo Masallaci Lokacin Huduba Yayi Sallahn Nafila, Amma Indai Yazo Da Wuri Ne, Kafin Lokacin Huduba, Yana Iya Yin Sallahn Nafilansa )

 وَكَذَلِكَ يُكْرَهُ لِلجَالِسِ أَنْ يَتَنَفَّلَ عِنْدَ الأَذَانِ الأَوَّلِ،
Hakanan ( An Karhanta ) Yin Sallahn Nafila Ga Wanda Yake Cikin Masallaci A Zaune, A Yayin Qiran Sallahn /raubabangida/ Na Farko.

 وَيُكْرَهُ حُضُوْرُ الشَّابَّةِ لِلجُمُعَةِ،
Hakanan An Karhanta Zuwa 'Yan Mata Zuwa Sallahn Juma'ah ( Amma Idan Sunje Ba Damuwa, Amma Wallahu A'alamu Ko Don Gudun 'Daukan Hankalin Maza A Wajen Sallahn Za'a Iya Karhantawa, Domin /raubabangida/ Wasu 'Yan,matan Da Samarin Zasu Samu Damar Yin Hira Na Soyayya Ko Aikata Wasu Abubuwa Da Shari'ah Ta Hana /raubabangida/ Ko Shari'ah Ta Haramta D.s )

 وَكَذَلِكَ السَّفَرُ بَعْدَ الفَجْرِ.
Hakanan ( An Karhanta ) Yin Tafiya Bayan Alfijir.
وَاللهُ أَعْلَمُ.
Wallahu A'alamu
Allah Shine Masani
Allah Shine Mafi Sani.
*

Masha Allah Alhamdulillahi
Wannan Shine Qarshen Babin, Wanda AL-SHEIKH AL-IMAM AL-ALIMU AL-ALAMATU ABDUL-BARIYI AL-ASHMAWIY RUFA'IYUN Allah Yaji Qansa Da Rahma Wallafa.
*
Abunda Muka Rubuta Dai-Dai Ubangiji Allah Ya Bamu Ladansa, Abunda Muka Rubuta Bisa Kuskure Ubangiji /raubabangida/ Allah Ya Gafarta Mana.
@@@@ @@@@ @@@@ @@@@

03 Rabi'ul Awwal 1448 Hijrah
16 August 2026 Miladiyyah
Ranar Lahadi
11am

marubuci

@raubabangida
Rabiu Alhaji Umar Babangida
BPM PAN PHM, CON, MVM, AUYO, YOLA-NORTH

Comments

Popular posts from this blog

TAQAITACCEN TARIHIN DAULAR AUYO

HAPPY BIRTHDAY TO YOU OUR DEAR FATHER, 13 APRIL

YAU SHEKARA GOMA DA RASUWA MAMANA