004 TAQAITACCEN BAYANI AKAN SALLAN JUMA'AH
@@@@ @@@@ @@@@ @@@@
بسم الله الرحمن الرحيم
والصلاة والسلام على أشراف أنبياء سيدنا ومولانا محمد النبي وعلى أزواجه أمهات المؤمنين وذريته وأهل بيته الطاهرين وصحابته الأكرمين وعلينا معهم أجمعين
@@@@ @@@@ @@@@ @@@@
Ina Qara Godewa Allah Bisa Kasantuwar Musulunci Addinina, Annabi Muhammad SAW Annabi Na, Al-qur'ani Da Hadisi Littatafaina Tsarkaka, Ka'aba Ash-sharifah Alqiblata, Malikiyyah Mazhabata, Ash'ariyyah Aqidata Ta Sunnah, Sufanci Matafiyata, Qadiriyyah Dariqata, Hausa Qabilata.
Aslm
Ya 'Yan,uwana Musulmai Maza Da Mata Manya Da Qanana Da Fatan Kowa Yana Qoshin Lafiya, Marasa Lafiyanmu Na Gida Da Na Asibiti Ubangiji Allah Ya Basu Lafiya, Masu Lafiya Kuma Allah Ya Qara Musu Lafiya, Iyayenmu Da Kakanayenmu Yayyunmu Da Qannanmu, Da Suka Rigamu Gidan Gaskiya Ubangiji Allah Yaji Qansu Yayi Musu Rahma, Muma In Tamu Tazo Allah Ya Sa Mu Cika Da Imani.
Ameen Summa Ameen
*** *** *** *** *** *** *** *** ***
Insha Allahu Cikin Wannan Rubutun Zamu 'Dan 'Dauko Taqaitaccen Bayani /raujimetawiy/ Dangane Da Sallan Juma'ah Daga Littafin Fiqhun Mazhabar Malikiyyah, Sanannen Littafin Da Kowa Yasanshi, Wato ISHMAWIY Wanda AL-SHEIKH AL-IMAM AL-ALIMU AL-ALAMATU ABDUL-BARIYI AL-ASHMAWIY RUFA'IYUN Allah Yaji Qansa Da Rahma Wallafa.
A Gurguje
In Bamu Manta Ba, A Kashi Na 3 Munce Insha Allahu Zamu Tashi A Inda /raubabangida/ Malam Yake Cewa :
وَأَمَّا الأَعْذَارُ الْمُبِيْحَةُ لِلتَّخَلُّفِ عَنْهَا
AMMA UZURAI WANDA SUKE HALATTATTU BARI ZUWA SALLAN JUMA'AH
فَمِن ذَلِكَ:
Yana Daga Cikin Haka
المَطَرُ الشَّدِيْدُ، وَالوَحْلُ الكَثِيْرُ،
Ruwan Sama Mai Tsanani, Da Laka/Ta6o Mai Yawa ( Abun Nufi : Inya /raubabangida/ Ya Kasance Misali : Tsakanin Garinku Ko Gidanku Da Masallacin Juma'ahn Akwai Ta6o/Laka Irin Wanda Idan Ka Shiga Zaka Maqale, Ko Zai Ba66ata /raubabangida/ Maka Kaya Da Jiki Kafin Ka Isa Masallacin Etc Toh Ka Zauna A Gida Kayi Azahar Naka, Hakanan Idan Ruwan Sama Ya Sauqo Kaman Bakin Kwarya /raubabangida/ Ruwan Bai Tsaya Ba, Kuma Babu Alaman Zai Tsaya, Nanma Zauna A Gida Kayi Azahar Naka.
وَالْمُجَذَّمُ الذِي تَضُرُّ رَائِحَتُهُ بِالجَمَاعَةِ،
Da Kuturu Wanda Warin ( Ciwonsa Na Kuturta ) Yake Cutar Da Mutane. ( Shima An Sauwaqe Masa Ya Zauna /raubabangida/ A Gida Yayi Sallansa Na Azahar )
وَالمَرَضُ، وَالتَّمْرِيْضُ ؛ بِأَنْ يَكُونَ عِنْدَهُ أَحَدٌ مِنْ أَهْلِهِ مَرِيْضًا، كَالزَّوْجَةِ وَالوَلَدِ وَأَحَدِ الأَبَوَيْنِ، وَلَيْسَ عِنْدَهُ مَن يَعُوْلُهُ، فَيَحْتَاجُ إِلى التَّخَلُّفِ لِتَمْرِيْضِهِ.
Da Mara Lafiya, Da Wanda Zai Tsaya Akan Marar Lafiyan ( Rashin Lafiya Mai Tsani Ake Nufi Da Wanda /raubabangida/ Zai Tsaya Akansa, An Dauke Musu Zuwa Sallan Juma'an, Su Sallan Azahar Nasu ) Anaso A Bar Mutum A Wajensa ( Shi /raubabangida/ Mara Lafiyan Wanda Zai Dinga Kula Dashi ) Daga Ahlinsa/Danginsa Kamar Matarsa, Ko 'Dansa Ko 'Daya Daga Cikin /raubabangida/ Iyayensa.
Ba'aso A Bar Shi ( Mara Lafiyan ) Shi Kadai Ba Kowa A Wajensa, Toh Shi Wanda Zai Tsaya Akan Marar Lafiyan Yana Buqatar Barin Zuwa Sallan Juma'ah ( Wato Anyi Masa Afuwan, Ya Zauna Yayi Sallar Azahar Nashi, Imma Suna Gida Ne, Imma Suna /raubabangida/ Asibiti )
*
وَمِن ذَلِكَ إِذَا احْتُضِرَ أَحَدٌ مِن أَقَارِبِهِ أَو إخْوَانِهِ.
Yana Daga Cikin Haka, Idan Daya Daga /raubabangida/ Cikin Makusantansa Ko 'Yan,uwansa Ya Gabato / Ya Halarto / Ya Mutu
قَالَ مَالِكٌ في الرَّجُلِ يَهْلِكُ يَوْمَ الجُمُعَةِ
Imam Malik Yace : Dangane Da Wanda Ya Halaka/ Ya Rasu A Ranar Juma'ah
فَيَتَخَلَّفُ عِنْدَهُ رَجُلٌ مِن إخْوَانِهِ يَنْظُرُ في شَأْنِهِ: لاَ بَأْسَ بِذَلِكَ
Toh Sai A Bar Mutum A Wajensa ( Shi Mamacin ) Daga Cikin 'Yan,uwansa /raubabangida/ Wanda Zai Kula Da Sha'anin Gawan ( 'Dan,uwan Nasu ) Toh Yin Hakan Babu Laifi
وَمِنْهَا لَو خَافَ عَلَى نَفْسِهِ مِن ضَرْبِ ظَالِمٍ أَوْ حَبْسِهِ أَوْ أَخْذِ مَالِهِ،
Daga Cikinta ( Wato Uzuran Da Suke Sanya Mutum Baein Zuwa Sallahn /raubabangida/ Juma'ah )
In Da Mutum Zaiji Tsoron Duka Daga Azzalumi, Ko Kuma Jin Tsoron Kameshi ( Something Like Kidnapping ) Ko Kwace Dukiyarsa ( Toh Wadannan/raubabangida/ Su Zauna A Gida Suyi Azahar Nasu )
( Abun Nufi Misali : Mutanen Da Suke Karkara Wadanda Basuda Masallacin Juma'ah A Qauyensu, Sai Sun /raubabangida/ Fito Izuwa Gari Da Yake Kusa Dasu, Toh A Hanya Inya Ya Kasance Za'a Samu Wadannan Matsaloli Su Taru A Qauyensu Su Gabatar Da Sallahr Azahar /raubabangida/ Insha Allahu )
وَكَذَلِكَ الْمُعْسِرُ يَخَافُ أَنْ يَحْبِسَهُ غَرِيْمُهُ عَلَى الأَصَحِّ..
Hakanan Talaka Da Yake Jin Tsoron Kada A Tsare/Kulleshi Saboda Bashin Da Ake Binsa.
( Mutum Ne Ya Kar6i Bashi Saboda Quncin Rayuwa Misali, Kuma Ya Tabbatar Da /raubabangida/ Inya Je Masallacin Juma'ahn Zasu Hadu, Kuma Insu Hadu Ba Makawa Zai Kulleshi, Toh Nan Ma Akace Shima Yayi Zamansa Ya Gabatar Da Sallahn /raubabangida/ Azahar. In Kuma 'Dan Cikin Gari Ne, Nan Kuma Baida Uzurin Qin Zuwa Sallahn Juma'ah, Saboda Masallatan Juma'ah Suna Da Yawa, Idan Mai Binka Bashi Yaje Masallacin Da Ya Saba Zuwa, Kai Kuma Sai Kaje Wani Masallacin Daban. Amma Hakan Ba Yana /raubabangida/ Nufin An Budewa Mutane Wata Qofar Bah, Don Haka A Kiyaye )
*
وَمِن ذَلِكَ الأَعْمَى الذِي لاَ قَائِدَ لَهُ،
Hakanan Makaho Wanda Baida 'Dan Jagora ( Kuma Bazai Iya Zuwa Masallacin Sallahn Juma'ah Ba, Shima An /raubabangida/ Masa Uzuri Yayi Sallan Azahar Nashi )
أَمَّا لَوْ كَانَ لَهُ قَائِدٌ، أَوْ كَانَ مِمَّن يَهْتَدِيْ لِلجَامِعِ بِلاَ قَائِدٍ، فَلاَ يَجُوْزُ لَهُ التَّخَلُّفُ عَنْهَا.
Amma Da Zai Kasance Yana Da 'Dan Jagora, Ko Ya Kasance Zai Iya Zuwa Ta ( Hanyar Jin Sawayen Qafafun /raubabangida/ Mutane Ko Suturun Mutane A Hanya, Inya Kasance Zai Iya Hakan ) Ba Tareda 'Dan Jagora Ba, Toh Ba Ya Kamata ( Ga Wannan /raubabangida/Makahon ) Ya Bar Zuwa Sallahn Juma'ahn.
*** *** *** *** *** *** *** *** ***
Masha Allah Alhamdulillahi Duka-Duka Anan Zan Tsaya, Insha Allahu Kuma A Kashi Na Qarshe Wato Kashi Na 5
Insha Allahu /raubabangida/ Zamu Tashi A Inda Malam RH Yake Cewa
ويحرم السَّفَرُ عِنْدَ الزَّوَالِ مِن يَومِ الجُمُعَةِ
@@@@ @@@@ @@@@ @@@@
23 Safar 1448 Hijrah
07 August 2026 Miladiyya
Ranar Juma'ah
5pm
marubuci
Abu Maryam Muhammad Rabiu Babangida Jimetawiy Bini Alhaji Umaru al-Auyowiy Bini Muhammad Bini Haruna
@raubabangida
Rabiu Alhaji Umar Babangida
BPM PAN PHM, CON, MVM, AUYO, YOLA-N
Comments
Post a Comment