TAQAITACCEN TARIHIN 11TH LAMIDO ADANAWA

DR. ALIYU MUSTAPHA MUHAMMAD
@@@@ @@@@ @@@@ @@@@
بسم الله الرحمن الرحيم
والصلاه والسلام على أشراف أنبياء سيدنا ومولانا محمد النبي وعلى أزواجه أمهات المؤمنين وذريته وأهل بيته الطاهرين وصحابته الأكرمين وعلينا معهم أجمعين
@@@@ @@@@ @@@@ @@@@

Ina Qara Godewa Allah Bisa Kasantuwar Musulunci Addinina, Annabi Muhammad SAW Annabi Na, Al-qur'ani Da Hadisi Littatafaina Tsarkaka, Ka'aba Ash-sharifah Alqiblata, Malikiyyah Mazhabata, Ash'ariyyah Aqidata Ta Sunnah, Sufanci Matafiyata, Qadiriyyah Dariqata, Hausa Qabilata.

Aslm
Ya 'Yan,uwana Musulmai Maza Da Mata Manya Da Qanana Da Fatan Kowa Yana Qoshin Lafiya, Marasa Lafiyanmu Na Gida Da Na Asibiti Ubangiji Allah Ya Basu Lafiya, Masu Lafiya Kuma Allah Ya Qara Musu Lafiya, Iyayenmu Da Kakanayenmu Yayyunmu Da Qannanmu, Da Suka Rigamu Gidan Gaskiya Ubangiji Allah Yaji Qansu Yayi Musu Rahma, Muma In Tamu Tazo Allah Ya Sa Mu Cika Da Imani.
Ameen Summa Ameen
Dr. Aliyu Musdafa ( Mustapha ) Shine Lamido Na 11 Na Masarautar Adamawa, Wanda Ya Kasance Daya Daga Cikin Sarakuna Mafi 'Daɗewa A Kan Karagar Mulki Kuma Mafi Tasiri A Tarihin Najeriya.
*** *** *** *** *** *** *** *** ***
1 - Haifuwa Da Farkon Rayuwa

Ranar Haifuwa : An Haife Shi A Shekara Ta 1922 A Birnin Yola.

Karatu: Ya Halarci Makarantar Firamare Ta Yola ( Yola Elementary School ) Da Kuma Makarantar Sakandare /raubabangida/ Ta Yola ( Yola Middle School ) Tsakanin Shekarar 1936 Zuwa 1943.

2 - Fara Aiki

A Shekara Ta 1943, Ya Fara Aiki A Hukumar Mulkin Mallaka Na Adamawa (Adamawa Native Authority ).

A Shekara Ta 1945, Aka Naɗashi Shugaban 'Yan Sanda Na Lardin Adamawa ( Chief of Police ) Tareda Bashi Sarautar Wali. Ya Shafe Shekaru /raubabangida/ Takwas Yana Gudanar Da Wannan Aiki.

3 - Hawa Kan Ragamar Sarauta

Bayan Tu6e Lamido Ahmadu Maigari, Aka Za6i Dr. Aliyu Mustapha /raubabangida/ A Matsayin Lamido Na 11 Na Adamawa A Ranar 26 Ga Yuli, 1953.

Gwamnan Mulkin Mallaka Na Birtaniya /raubabangida/ Na Wancan Lokacin, Sir Bryan Sherwood-Smith, Shine Ya Mika Masa Sandar Girma.

4 - Gudunmawa Da Zamani

Tsawon Mulki : Yayi Mulki Na Tsawon Shekaru 57 ( 1953–2010 ).

Shugabannin Ƙasa : A Tsawon Mulkinsa, Yayi Aiki A Qarƙashin Shugabannin Qasa Guda 13 A Najeriya.

Muqamai Da Gudunmawa:

Ya Kasance Mamba A Majalisar Sarakuna Ta Arewacin Najeriya ( Northern House Of Chiefs ) Da Majalisar /raubabangida/ Jihohi Ta Qasa ( National Council of States ).

Ya /raubabangida/ Zama Shugaban Majalisar Sarakuna Na Jihar Gongola ( Lokacin Da Aka Qirqire Ta A 1976 ), Daga Baya Kuma Na Jihar Adamawa.

Zaman Lafiya Da Haɗin Kai : An San Shida Kiyaye Lafiya, Adalci, Da Kuma Samar Da Zaman Tare Tsakanin /raubabangida/ Qabilu Da Addinai Daban-Daban A Cikin Masarautar.

Ayyukan Cigaba: Ya Sake Gina Masallacin Tarihi Na Modibbo Adama /raubabangida/ Tare Da Kafa Gidan Tarihi Na Fombina Museum A Cikin Faɗadar Sarki.

5 - Rasuwa

Dr. Aliyu Mustapha Ya Rasu A Ranar 13 Ga Maris, 2010 Yana 'Dan Shekara 88. Ubangiji Allah Yaji Qansa Yayi Masa Rahma.

Ɗansa Alhaji Muhammadu Barkindo Aliyu Mustapha, Shine Ya Gajeshi /raubabangida/ A Matsayin Lamidon Adamawa Na 12.
( Ubangiji Allah Yaja Zamanin Sarkinmu, Ya Qara Lafiya Da Nisan Kwana )

@raubabangida
Rabiu Alhaji Umar Babangida
BPM PAN PHM, CON, MVM, AUYO, YOLA-N

Comments

Popular posts from this blog

TAQAITACCEN TARIHIN DAULAR AUYO

HAPPY BIRTHDAY TO YOU OUR DEAR FATHER, 13 APRIL

YAU SHEKARA GOMA DA RASUWA MAMANA