007 TAQAITACCEN BAYANI AKAN AURE, SAKI, BIKO, ZIHARI, ILA'I, LI'ANI, KUL'I DA KUMA SHAYARWA



@@@@ @@@@ @@@@ @@@@
بسم الله الرحمن الرحيم
والصلاة والسلام على أشراف أنبياء سيدنا ومولانا محمد النبي وعلى أزواجه أمهات المؤمنين وذريته وأهل بيته الطاهرين وصحابته الأكرمين وعلينا معهم أجمعين
@@@@ @@@@ @@@@ @@@@

Ina Qara Godewa Allah Bisa Kasantuwar Musulunci Addinina, Annabi Muhammad SAW Annabi Na, Al-qur'ani Da Hadisi Littatafaina Tsarkaka, Ka'aba Ash-sharifah Alqiblata, Malikiyyah Mazhabata, Ash'ariyyah Aqidah Ta Sunnah, Sufanci Matafiyata, Qadiriyyah Dariqata, Hausa Qabilata.

Aslm
Ya 'Yan,uwana Musulmai Maza Da Mata Manya Da Qanana Da Fatan Kowa Yana Qoshin Lafiya, Marasa Lafiyanmu Na Gida Da Na Asibiti Ubangiji Allah Ya Basu Lafiya, Masu Lafiya Kuma Allah Ya Qara Musu Lafiya, Iyayenmu Da Kakanayenmu Yayyunmu Da Qannanmu, Da Suka Rigamu Gidan Gaskiya Ubangiji Allah Yaji Qansu Yayi Musu Rahma, Muma In Tamu Tazo Allah Ya Sa Mu Cika Da Imani.
Ameen Summa Ameen.
*
A Gurguje Insha Allahu Zamu 'Dan Ta6a Bayani Akan AURE, SAKI ETC
Daga /raujimetawiy/ Littafin Da Ake Qira Da RISALA Wanda 
Abu Muhammad Abdullahi Bini Abiy Zaideen Al-Qirawaniy RH Ya Wallafa.
*
A Gurguje
In Bamu Manta Ba, A Kashi Na Shida Munce Insha Allahu Zamu Tashi A /raujimetawiy/ Malam Yake Cewa :

وَنِكَاحُ التفْوِيضِ جَائِزُُ
Auren Tafwidi Ya Halatta
وَهُوَ أَنْ يَعْقِدَاهُ ولاَ يَذْكُرَانِ صَدَاقََا
Shine ( Auren ) Da Ake 'Daurawa Ba Tareda /raujimetawiy/ An Ambaci Sadaki Ba.
( Hakan Yana Faruwa, Kaga An 'Daura Aure, Ga Wakilin Ango Ga Waliyin Amarya, Ga Shaidu Dade Sauran Mutane /raujimetawiy/ A 'Daura Aure Ayi Siga Komai Da Komai, Amma Bakaji An Ambaci Sadaki Ba )
ثُمَّ لاَ يَدْخُلُ بِهَا حَتَّى يَفْرِضَ لَهَا
( Idan /raujimetawiy/ Hakan Ta Faru, An Daura Aure Ba Tareda An Ambaci Sadaki Ba, Toh Mijin ) Bazai Sadu/Jima'i Da Ita, Har Sai An Ambata Mata Sadakinta,
فَإِنْ فَرَضَ لَهَا صَدَاقَ المِثْلُ لَزِمَهَا
Idan An Ambata Mata Mata Sadakinta /raujimetawiy/ Kwatankwacinta, Toh Mijin Yana Iya Saduwa/Jima'i Da Ita,
( Abun Nufi Da Kwatankwacinta Shine : Mata Suna Nan Class Class Ne, Akwai 
- Class Na 'Ya'yan Talakawa
- Class Na 'Ya'yan Masu Kudi
- Class Na 'Ya'yan Sarauta
Idan 'Yar Talakawa Ce, Toh Sai A Bada Sadakinta /raujimetawiy/ Yadda Ake Bawa Yaran Talakawa,
Idan 'Yar Masu Kudi, Itama Haka,
Idan /raujimetawiy/ 'Yar Sarauta Ce, Itama Haka )
وَإِنْ كَانَ أَقَلَّ فَهِيَ مُخَيَّرَةُُ، فَإِنْ كَرِهَتْهُ فُرِّقَ بَيْنَهُمَا
( Idan Aka Ambata Mata Sadakin ) Sadakin Yayi Qasa Yayi Qaranci ( Bisa Class/Level Na Ta ) Toh Tana Da Za6i, Idan Ta Qi ( Ta Raina, A Matakin /raujimetawiy/ Class/Level Na Ta ) Za'a Raba Tsakaninsu,
( Amma Kafin /raujimetawiy/ Kafin Rabawan Ya Kamata Aji Ta Wajensa Shin Zai Iya Qarawa, Ko A Take Ko Zuwa Wani 'Dan Lokaci, Ko Kuma A Duba /raujimetawiy/ Akwai Wani Daga Dangi Dazai Cika Masa Etc, Idan An Samu Toh Shikenan, Idan Ba'a Samu Ba, Ita Kuma Taga Bazata Iya Haqura Ba, Sai A Raba Tsakanin Nasu )
إِلاَ أَنْ يُرْضِيَهَا أَوْ يَفْرِضَ لَهَا صَدَاقَ مِثْلُهَا فَيَلْزَهُمَا
Idan Ta Yarda Toh Shikenan, Koh Kuma Aka Ambata Mata Sadakin Dai-Dai Kwatankwacinta, Ya Lazimcesu ( Shikenan Komai Yayi Dai-Dai, Suna Iya Saduwa/Jima'i )

*

وَإِذَا ارْتَدَّ أَحَدُ الزَّوْجَيْنِ انفَسَخَ النِّكَاحُ بِطَلاَقِِ وقَدْ قِيْلَ بِغَيْر طَلاَقِ
Idan 'Daya Daga Cikin Ma'aurata ( Miji Ko Mata, Wani Daga Cikinsu ) Yayi /raujimetawiy/ Ridda, Aurensu Ya 'Baci Da Saki, A Wani Zance Bada Saki Ba, Auren Ya 'Baci,
وَإِذَا أَسْلَمَ الكَافِرَانِ ثَبَتَا عَلَى نِكَاحِهِمَا
Idan /raujimetawiy/ Kafirai Guda Biyu Suka Musulunta ( Mata Da Miji Duka Suka Musulunta Lokaci 'Daya ) Toh Aurensu Yana Nan ( Bai 'Baci Ba, /raujimetawiy/ Ba Sai An Sake 'Daura Wani Auren Ba )
وَإِنْ أسْلَمَ أَحْدُهُمَا فَذَلِكَ فَسْخُُ بِغٕيْرِ طَلاَقِِ 
Idan 'Daya Daga Cikinsu Ya Musulunta /raujimetawiy/ Za'a Warware Auren Ba Tareda Saki Ba,
فَإِنْ أَسْلَمَتْ هِىَ كَانَ أَحَقَّ بِهَا إِنْ أَسْلَمَ فِى الْعِدَّةِ
Idan Matar Ne Ta Musulunta, Mijin Shine /raujimetawiy/ Mafi Cancanta Da Ita Idan Ya Musulunta Tana Cikin Idda, ( Idan Kuma Ta Gama Idda Bai /raujimetawiy/ Musulunta Ba, Toh Aurensu Ya Warware.
فَإِنْ أَسْلَمَ هُوَ وَكَانَتْ كِتَابِيَّةََ ثَبَتَ عَلَيْهَا
Idan Kuma Shine ( Shi Mijin ) Ya Musulunta, /raujimetawiy/ Matar Kuma Ita Ahlul Kitabi Ne ( Bayahudiya Ko Kirista, Toh Mijin ) Ya Tabbata A Gareta ( Aurensu Na Nan )
فَإِنْ كَانَتْ مَجُوسِيَّةُُ فأَسْلَمَتْ بَعْدَهُ مَكَانَهَا كَانَا زَوْجَيْنِ
Idan /raujimetawiy/ Kuma Matar Ta Kasance Majusiya ( Masu Bautar Dodo, Gumaka Ko Aljanu ETC ) Sai Ta Musulunta A Bayansa ( Wato Bayan Musuluntan Mijin ) Toh Sun Kasance /raujimetawiy/ Ma'aurata ( Aurensu Na Nan )
وَإِنْ تَأَخَرَ ذَلِكَ فَقَدْ بَانَتْ مِنْهُ
Idan Kuma /raujimetawiy/ Ta Jinkirta ( Musuluntan, Ba Ta Musulunta Tsawon Lokaci )Toh Ta Nisanta Daga Gareshi ( Aurensu, Ya Wargaze )
وَإِذَا أَسْلَمَ مُشْرِكُُُ وَعِنْدَهُ أَكْثَرَ مِنْ أَربَعِِ فَلْيَخْتَرُ أَرْبَعََا، وَيُفَارِقُ بَاقِيَهُنَّ
Idan Mushriki ( Kafiri Mai Bautan Dodanni, Gumaka Etc ) Ya Musulunta Ya Kuma Kasance A Wajensa Yana Mata Sama Da Guda Hudu, /raujimetawiy/ Toh Za'a Bashi Za6i, Ya Za6i Mata Guda Hudu, Sauran Kuma Za'a Rabasu ( Domin Musulunci Ya Hana Auren Mata Sama /raujimetawiy/ Da Guda Hudu )
*
وَمَنْ لاَعَنَ زَوْجَتَهُ لَمْ تَحِلَّ لَهُ أَبَدََا
Wanda Yayi /raujimetawiy/ Li'ani/RantsuwanTsinuwa Da Matarsa Toh Bata Halatta A Gareshi ( Su Sakeyi Aure ) Har Abada ( Bayanin Li'anin /raujimetawiy/ Yana Gaba Kadan, Zamu Je Kansa Insha Allahu )
وَكَذَلِكَ الَّذٓى يَتَزَوَجُ الْمَرْأَةَ فِى عِدَّتِهَا، وَيَطَؤُهَا فِى عدَّتِهَا.
Hakan Wanda Ya Auri Mace Tana Cikin Idda ( Imma Idda Na Saki, Ko Idda Na /raujimetawiy/ Rasuwa Wato Takaba ) Har Takai Ga Ya Sadu/Jima'i Da Ita ( Toh, Suma Babu Aure.
Dangane Da Wannan Maganar Idan Muka Koma 
MINHAJUL MUSLIM
Shafi Na 343 
Bugun Darul Fikr
Ya Kawo Bayani Kamar Haka
النكاح فى العدة
Aure A Cikin Idda
وهو أن يتزوج الرجل المرأة المعتدة من طلاق أو وفاة
Shine : Mutum Ya Auri Mace Mai Yin Idda /raujimetawiy/ Daga ( Imma ) Idda Na Saki Ko Idda Na Takaba
فهذا النكاح باطل ' وحكمه أن يفرق بينها لبطلان العقد وثبت للمرأة الصداق إن كان قد خلا بها
Wannan Auren 'Batacce Ne, Hukuncinsa Shine Za'a Raba Tsakaninsu, Saboda 'Bacin Qulla Auren, /raujimetawiy/ ( Idan Har Ta Kai Ga Mijin ) Ya Sadu/Jima'i Da Ita, Toh Taci Sadakinta
ويحرم عليه أن يتزوجها بعد انقضاء عدتها عقوبة له
Hakanan ( Matan ) Tana Haramta Gareshi ( Ya Aureta ) Bayan Ta Gama Iddan, ( Hukuncin Hakan ) Domin Ya Uquba Gareshi ( Wato Ya Zamo /raujimetawiy/ Jan Kunne Gareshi, Ya Zamo Caution A Kiyaye Ayi Taka Tsan-Tsan, Ba Iya Shi Kadai Ba /raujimetawiy/ Da Dukkan Kowa Ma )
وذلك لقوله تعالى : { وَلاَ تَعْزِمُوا عُقْدَةَ النِّكَاحِ حَتَّى يَبْلُغَ الكِتَبُ أَجَلَهُ }
Hakanan Fadin Allah Madaukakin Sarki :
( Kada Ku Qudurci/Niyyan 'Daura Aure Har Sai Littafi Ya Cika Ajalinsa/Lokacinsa ( Wato Har Sai Anyi Idda An Gama ) } Suratul Baqarati Aya;Ta 235
*
ولاَ نِكَاحَ لِعَبْدِ وَلاَ لِأَمَةِِ إِلاَ أَنْ يَأَذَنَ السَّيِّدُ
Bawa Da Baiwa Bazasu Daurawa ( Kansu Da Kansu ) Aure Ba, Saida Izinin /raujimetawiy/ Shugabansu.
*
وَلاَ تَعْقِدُ امْرَاةُُ وَلاَ عَبْدُُ وَلاَ مَنْ عَلَى غَيْرِ دِينِ الإِسْلاَمُ نِكَاحَ امْرَأَةِِ
Mutum Bawa ( Wanda Ba 'Yantacce Ba ) Da Wanda Yake Ba Abisa Addinin Musulunci ( Wanda Ba Musulmi Ba, /raujimetawiy/ Baya Yuyuwa ) Su Aurar Da Mace.
*
وَلاَ يَجُوزُ أَنْ يَتَزَوَّجَ الرّجُلُ امْرَأَةََ لِيُحِلَّهَا لِمَنْ طَلَّقَهَا ثَلاَثَا وَلاَ يُحِلُّهَا ذَلِكَ
Baya Halatta Mutum Ya Auri Mace Wacce Mijinta Ya Saketa Saki Uku Domin /raujimetawiy/ Ya Halatta Ta ( Ga Tsohon Mijinta, Auren Kisan Wuta ) Koda Yayi Hakan Ma Ya Aureta ) Bai Halatta Ba.

Har Yanzu Dai Muna 
MINHAJUL MUSLIM
Shafi Na 343
Bugun Darul Fikr
Zamu Ga /raujimetawiy/ Malam Mai Littafi Yana Cewa

٣ - نكاح المحلل
Auren Kisan Wuta
وهو أن تطلق المرأة ثلاثا ، فتحرم على زوجها به لقوله تعالى { فَلاَ تَحِلُّ لَهُ مِنْ بَعْدُ حَتَّى تَنْكِحَ زَوْجََا غَيْرَهُ }
Shine : A Saki /raujimetawiy/ Mace Saki Uku, ( Idan Miji Ya Saki Matarsa Saki Uku Toh ) Ta Haramta Gareshi ( Yayi Bikonta Ko Ya Sake Aurenta ) Saboda Allah Madaukakin /raujimetawiy/ Sarki { Bata Halatta Gareshi Daga Baya ( Saki Uku ) Har Sai Ta Auri Wani Mijin } Suratul Baqara Aya Ta 230
( Sannan Idan Ma Ta Auri Wani Mijin /raujimetawiy/ Sai Mijin Ya Dandaneta Itama Ta Dandaneshi, Wato Sai Sunyi Jima'i )
فيتزوجها ٱخر قصد أن يحلها لزوجها الأول فهذا النكاح باطل لقول ابن مسعود " لَعَنْ رَسُولّ اللَّه صَلَّى اللَّهُ عَلَيْهٌ وسَلَّمَ المحلَّل وَالمحلَّلَ لَهّ. رواه الترمذى
Wato Shine Wani Mutum Dabam Ya Aureta Yana Mai Qudurcewa/Niyyan Halatta Ta /raujimetawiy/ Ga Mijinta Farko, Toh Wannan Auren 'Batacce Ne ( Hakan Tana Faruwa Mutum Ya Saki Matarsa Saki Uku, Yaje Ya Samu Wani Su Shirya Ya Bashi Kudi Akan Ya Aureta Bayan Wani Lokaci Ya Sakota Shikuma /raujimetawiy/ Ya Sake Auranta, Dade Makamantan Haka, Toh Ko Hakan Ta Faru Auren 'Batacce Ne, Kuma Hadisi Yazo ) Daga Ibnu Mas'ud Yace : Manzon Allah S.A.W Ya Tsinewa Mai Halattawa Da Wanda Za'a Halatta Masa ( Wato Wanda Zaiyi Auren Kisan Wutan Da Wanda Za'ayi Masa Auren /raujimetawiy/ Kisan Wutan ). Rawahul Tirmizi
وحكم هذا النكاح أن يفسخ ولا تحل به الزوجة لمن طلقها ثلاث،
Hukuncin Wannan Auren Shine Za'a 'Batashi, /raujimetawiy/ Kuma Matan Bata Halatta Ga Mijin Nata Da Ya Saketa Saki Ukun
ويثبت المهر للزوجة إن وطئت، ثم يفرق بينهما
Idan /raujimetawiy/ Mijin Ya Sadu/Jima'i Da Matar Toh Taci Sadakinta, Sannan Kuma Za'a Raba Tsakaninsu.
@@@@ @@@@ @@@@ @@@@

Masha Allahu Duka-Duka Anan Zan Tsaya Insha Allahu A Kashi Na Takwas Kuma Saimu Tashi A Inda Malam /raujimetawiy/ Yake Cewa :
ولا يجوز نكاح المحرم لنفسه ولا يعقد نكاحا لغيره
@@@@ @@@@ @@@@ @@@@

27 Zhul Hijjah 1447 Hijrah
12 June 2026 Miladiyya
Ranar Juma'ah
8am
marubuci
Abu Maryam Muhammad Rabiu Jimetawiy Bini Alhajj Umar al-Auyowiy Bini Muhammad Bini Haruna

( Wanda Akafi Sani Da )

@raujimetawiy
Rabiu Alhaji Umar Jimetawiy,
BPM PAN PHM, CON, MVM, AUYO, YOLA-N

Comments

Popular posts from this blog

TAQAITACCEN TARIHIN DAULAR AUYO

HAPPY BIRTHDAY TO YOU OUR DEAR FATHER, 13 APRIL

YAU SHEKARA GOMA DA RASUWA MAMANA